Abba Ibrahim Wada" />

PSG Ta Shirya Fafatawa Da Barcelona A Yau

PSG

A yau Talata kungiyar kwallon kafa ta Paris St Germain za ta ziyarci abokiyar hamayyar ta kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, domin buga wasan farko zagaye na biyu a gasar cin kofin zakarun turai na Champions League.

Barcelona ta kawo wannan matakin ne, bayan da ta yi ta biyu a rukuni na bakwai da maki 15, iri daya da na Juventus wadda ta ja ragamar rukunin nasu ita kuwa Paris St Germain maki 12 ta hada iri daya da na RB Leipzig, amma kungiyar ta Faransa ita ce kan gaba a rukuni na takwas.

PSG ta samu kwarin gwiwar zuwa filin wasa na Nou Camp, bayan da ranar Asabar ta doke kungiyar Nice da ci 2-1 a gasar Ligue 1 bayan da dan wasan gaba na kungiyar Julian Dradler da kuma Moise Kean suka ci wa PSG kwallayen, kuma wasa na hudu a dukkan karawa da ta ci a jere kawo yanzu.

Sai dai kuma dan kwallon Brazil, Neymar ba zai buga fafatawar ba, sakamakon jinya da yake yi daman Neymar kan samu matsala a irin wannan mataki, ko dai ya yi laifi a hukunta shi ko kuma rauni ya hana shi buga fafatawar.

Shi ma dan kasar Argentina, Angel Di Maria na jinya, ba zai buga gumurzun da PSG za ta yi a Nou Camp ba ranar Talata sannan PSG ta yi nasara a wasa shida a Ligue 1 da ta kara karkashin Pochettino, bayan cin uku daga fafatawa bakwai a shekarar 2020 karkashin tsohon kociyan kungiyar Thomas Tuchel.

Wannan ne karon farko da kungiyoyin za su hadu tun bayan da Barcelona ta casa PSG 6-1 a gasar Champions League ranar 8 ga watan Maris din shekara ta 2017 bayan da tun farko PSG ce ta doke Barcelon da ci 4-0 a wasan farko da suka buga a Faransa ranar Talata 14 ga watan Fabrairun 2017.

Neymar, ya samu rauni wanda hakan yasa ba zai fafata wasan cin kofin zakarun turan ba da kungiyar zata fafata da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona a mako mai zuwa sannan Neymar yaji ciwo ne a wasan daya buga a gasar rukuni-rukuni na kasar Faransa kuma likitocin kungiyar sun bayyana cewa dan wasan zai iya yin makonni hudu yana jiyya kuma ya fita daga cikin jerin ‘yan wasan da zasu fafata da Barcelona.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da aka tabbatar da cewa dan wasa Angel Di Maria ya samu ciwo kuma ba zai fafata wasan farko ba da kungiyoyin zasu fafata sai dai ana ganin zai buga wasa na biyu a cewar likitocin kungiyar.

Shi ma dan wasan kungiyar Barcelona Philliph Coutinho ba zai fafata wasannin da kungiyoyin biyu zasu buga ba sakamakon ciwon daya samu a kwanakin baya sai dai daman ya dade yana jiyya kuma Barcelona ta saba buga wasa babu shi sannan shima dan wasa Ansu fati har yanzu babu tabbas din ko zai iya buga wasan.

A kwanakin baya ne tauraron dan wasa Neymar ya rattaba hannu kan kara wa’adin zamansa tare da kungiyar PSG na tsawon shekaru hudu, abinda ke nufin sai a shekarar 2026 za su raba gari musamman idan kungiyar tana kokari.

Kafin matakin na Neymar dai, an sha alakanta dan wasan da sauyin sheka zuwa tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona, la’akari da cewar, yayi jinkirin tsawaita wa’adin yarjejeniyar sa da kungiyar ta PSG da ke shirin karewa a shekarar badi ta shekara ta 2022 saboda yana son komawa Barcelona.

Tun bayan sauyin shekarsa zuwa gasar League 1 ta kasar Faransa a shekarar 2017 daga La Liga, Neymar ya taimaka wa PSG wajen lashe kofuna 9 a Faransa, ciki har da na gasar ta League 1 guda 3.

A shekarar data gabata kungiyar kwallon kafa ta Barcelona taso daukar dan wasan sai dai daga baya kuma PSG ta bayyana cewa ba zata sayar da dan wasan ba duk da cewa tana bukatar kudin kashewa a kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa.

Neymar dai yasha bayyana burinsa na barin kungiyar sakamakon gazawar kungiyar wajen lashe gasar cin kofin zakarun turai wanda hakan yasa kungiyar tayi masa alkawarin cewa zata sayo manyan ‘yan wasan da zasu iya lashe mata kofin.

Sabuwar yarjejeniyar da Neymar ya sanya zata sanya manyan ‘yan wasa su koma kungiyar ciki har da Messi wanda kungiyar take zawarci bugu da kari dan wasa Kylian Mbappe ana zaton zai amince ya ci gaba da zaman kungiyar.

Exit mobile version