Dan wasan gaban Amurka Christian Pulisic na dab da kammala cinikin yuro miliyan 20 daga Chelsea zuwa AC Milan.
Pulisic, mai shekaru 24, yana gab da barin Stamford Bridge kuma ana sa ran a duba lafiyarsa a Milan a wannan makon.
Ya koma Chelsea ne daga Borussia Dortmund a kan fam miliyan 57.6 a shekarar 2019 wanda ya sa ya zama dan wasa mafi tsada daga Arewacin Amurka.
Pulisic ya jefa kwallaye 26 a wasanni 145 da ya buga ma Chelsea kuma ya buga wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai na 2021 da suka doke Manchester City.
Komawarshi zuwa Serie A na nufin zai hadu da tsohon abokin wasansa a Chelsea Ruben Loftus-Cheek, wanda shi ma ya koma Milan a bazara.
A halin da ake ciki, dan wasan gaba na Chelsea David Datro Fofana, mai shekara 20, ya koma Union Berlin a matsayin aro na tsawon kakar wasa ta bana.
Chelsea ta raba gari da manyan yan wasanta a kakar bana da suka hada da Kai Havertz zuwa Arsenal, Mateo Kovacic da zai koma Manchester City da kuma Mason Mount wanda ya koma Manchester United.
Cesar Azpilicueta ya koma Atletico Madrid, yayin da sauran yan wasan Kalidou Koulibaly ya tafi Al-Hilal, Edouard Mendy ya koma Al-ittihad da kuma N’Golo Kante wanda shima ya koma Al-Ittihad.