• English
  • Business News
Sunday, October 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Putin Ya Fita Daga Raina – Trump

by Rabi'u Ali Indabawa and Sulaiman
3 months ago
Putin

Donald Trump ya ce Vladmir Putin na Rasha ya sare masa, kamar yadda ya shaida wa BBC a tattauna ta musamman ta wayar tarho.

Shugaban na Amurka ya amsa tambaya lokacin da aka tambaye shi ko ya yarda da shugaban Rasha, ya yi martani cewa: ”Babu wanda na yarda da shi.”

  • Tarihin Yadda Cinikin Bayi Ya Fara A Nahiyar Afirka (6)
  • Wace Kasa Ce Take Son Zama “Kasa Ta Uku Mai Tsaro” A Wurin Amurka?

Trump na wadannan bayanai ne sa’o’i bayan ya sanar da shirin aike makamai ga Ukraine da gargadin lafta haraji kan Rasha muddin taki cimma yarjejeniyar tsagaita wuta nan da kwanaki 50.

A tattaunawar da ta tabo abubuwa daban-daban daga ofishinsa, shugaban ya nuna yana tare da Nato, wanda a baya yake suka, tare da bayyana cikakken goyon-bayan ayyukanta na tsaro.

Shugaban ya bada damar tattaunawa da shi na mintina 20, bayan BBC ta tuntube shi domin tsokaci kan cika shekara guda da kokarin hallaka shi a Butler da ke, Pennsylbania.

LABARAI MASU NASABA

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

Da aka tambaye shi kan ko tsallake rijiya da baya a harin da aka kai masa ya sauya masa rayuwa, Trump ya ce baya son ya rinka yawan tuna wa da batun.

“Ya ce ba na son tunanin ko lamarin ya sauya ni, “In ji Trump. Zama ana nazari a kai, a cewarsa “na iya sauya mun rayuwa.”

Bayan ganawa da shugaban Nato Mark Rutte a fadar White House, shugaban ya yi amfani da damar da ya samu wajen bayanai da nuna takaicinsa da shugaban Rasha.

Trump ya ce ya yi tunanin za a cimma yarjejeniya a kan teburi da Rasha amma sai gashi an yi zama hudu ba a daidaita ba.

A lokacin da BBC ta yi masa tambaya idan hakan na nufi ya fita batun Putin, shugaban ya yi martani: ”Ina takaici kuma ya sare mun, amma dai ban kammala da shi ba. Amma dai ya bata mun rai.”

Da aka tambaye shi kan ko wace dabara zai yi amfani da ita wajen tursasa wa Bladimir Putin ya ”daina zub da jini” shugaban na Amurka ya ce, “Muna kokarin cimma hakan.”

“Za mu samu fahimtar juna, iya abin da zance kenan, kuma ina ganin muna hanyar cimma hakan,’ kuma shi da kansa ba zai sake rusa gini a Kyib ba.”

Sannan tattaunawar ta ci gaba a kan Nato, wanda a baya shugaba Trump ya sha caccaka a matsayin ”mara amfani”.

Da aka tambaye shi kan ko har yanzu yana kan wannan batu, ya ce, “A’a. Ina ganin a yanzu Nato ayyukanta sun inganta,” saboda hadakar, na ”biyan hakokin da ke wuyanta”.

Ya ce yana da yakinin hada hannu tare, saboda hakan na nufin kananan kasashe na iya kare kansu daga manyan kasashe.

An tambaye Trump kan makomar Burtaniya a duniya, sai ya ce yana ganin ”kasa ce mai kyau”, kuma yana da kadarori a kasar”.

Ya ce yana da anniyar kai ziyara a karo na biyu Burtaniya cikin watan Satumba wannan shekara.

Da aka masa tambaya me yake son cimma a ziyarar, Trump ya ce, “Ina son na samu lokaci mai armashi da girmama Sarki Charles, saboda mutumin kirki ne.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum
Manyan Labarai

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025
“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”
Labarai

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

October 26, 2025
Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano
Manyan Labarai

Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

October 26, 2025
Next Post
An Yi Taron Farko Na Shugabannin Matasa Na Dandalin Zaman Lafiya Da Tsaro Na Sin Da Afirka

An Yi Taron Farko Na Shugabannin Matasa Na Dandalin Zaman Lafiya Da Tsaro Na Sin Da Afirka

LABARAI MASU NASABA

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

October 26, 2025
Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025
Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

October 26, 2025
“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

October 26, 2025
Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

October 26, 2025
Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Gwamnati Na Shekarar 2025, Dakta Zacch Adedeji

October 26, 2025
An Yi Taron Tattaunawa Mai Taken “Shugabancin Duniya Da Samun Wadata Tare A Yankin Asiya Da Pasifik” A Beijing

An Yi Taron Tattaunawa Mai Taken “Shugabancin Duniya Da Samun Wadata Tare A Yankin Asiya Da Pasifik” A Beijing

October 26, 2025
Sin Da Amurka Sun Cimma Matsaya Dangane Da Tsare-Tsaren Warware Batutuwan Cinikayya Da Suke Mayar Da Hankali A Kai

Sin Da Amurka Sun Cimma Matsaya Dangane Da Tsare-Tsaren Warware Batutuwan Cinikayya Da Suke Mayar Da Hankali A Kai

October 26, 2025
Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

October 26, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.