Dan wasan gaba kuma kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Argentina, Lionel Messi, ya yabawa ‘yan wasan kasarsa kan nasarar da suka yi a wasan da suka yi da kasar Croatia.
Kyaftin din ya bayyana cewa, rashin nasarar da suka samu a wasansu na farko da kasar Saudiyya ne ya kara wa ‘yan wasan kasarsa kaimi a gasar cin kofin duniya na 2022. Kasar Saudiyya ta lallasa Argentina ne da ci 2 da 1.
A ranar Lahadi mai zuwa ne, kasar Argentina za ta kara da France ko Morocco bayan Argentina ta samu nasarar zuwa wasan karshe a wasanta da kasar Croatia inda ta lallasa Kasar da 3 da nema a filin wasa na Lusail a ranar Talatar da ta gabata.
Talla