Idan kana matukar son cin zabe a Nijeriya ba sai ka rika sauya sheka daga wannan jam’iyyar zuwa wancen. Babu wanda ya taba yin haka kuma ya cin zabe a Nijeriya tun lokacin da Turawan mulkin mallaka suka hada yankunan kasar nan a 1914.
Za a iya yin haka a matakin yanki da jiha, musamman a yankin da ke da dimbin kabilu. Amma a tarayya, mutum zai iya shan kasa idan ya yi hakan.
- Bayan Cinnawa Masallaci Wuta, Mutane 11 Sun Rasu A Kano
- Zanga-zangar Karin Kudin Wuta: Gwamnati Ta Shelanta Matakin Da Za Ta Dauka
Wadanda suke biyayya ga jam’iyyunsu ne kadai suka iya lashe zaben shugaban kasa ko na Firiminista a Nijeriya. Jam’iyyunku na iya shiga yin kwance ta hadewa da wata jam’iyya, ko ta sauya sunanta kuma mutum ya ci gaba da zama a cikinta. Amma a lokacin da ka bar jam’iyyaka ka kuma wata, mutane su ma za su bar ka.
Ko mai zai faru a cikin jam’iyyarka, ka zauna domin a warware lamarin. Ka tabbatar da kanka a can. Ka kasance mai gwagwarmaya wajen daga darajar jam’iyyarka. Idan har ba z aka iya jagorantar jam’iyyarka wajen warware matsaloli ba, to ba za ka iya shawo kan ra’ayin masu jefa kuri’a ba kan kabilanci na tunanin za ka iya fitar da kasa daga matsaloli.
Tafawa Balewa ya kasance dan jam’iyyar mutanen arewa. Bai taba sauya jam’iyya ba. Shagari dan jam’iyyar National Party of Nigeria, wanda ta koma jam’iyyar mutanen arewa. Bai taba sauya jam’iyya ba.
Obasanjo da Yar’adua da Jonathan dukkaninsu sun kasance ‘ya’yan jam’iyyar PDP. Ba su taba canza jam’iyya ba.
Buhari ya kasance dan jam’iyyar APP, wacce daga baya aka sauya mata suna zuwa ANPP. Daga karshe jam’iyyar ta rarrabu, kuma Buhari ya kasance a jam’iyyar CPC, a 2013, jam’iyyar ta hade da sauran jam’iyyu wanda aka samu jam’iyyar APC.
Tinubu ya kasance dan jam’iyyar SDP, wanda Abacha ya rushe a 1993. Bayan haka, ya taimaka wajen kafa jam’iyyar AD, wanda ta hade da sauran jam’iyyu aka samu ACN a 2006. ACN ta hade da sauran jam’iyyu aka samu jam’iyyar APC a 2013.
Ya kamata ‘yan siyasan Nijeriya su dauki darashi da abun da ya faru a baya. Mafi kyan hasashe a yi da abin da ya gabata. Daga yanzu zuwa 2027, duk dan siyasan da ya bar jam’iyyarsa zuwa wata jam’iyya ba tare da an yi hadaka ba, to yana taba wa kansa lokaci da kudinsa ne idan har ya tsaya takarar shugaban kasa.
Duk kasar da ke kokarin samun daidaiton siyasa ba za ta iya samun shugaba da yake faman samun hankalinsa da na daidaituwar siyasa ba.
Kasar da ke mafa da gwagwarmayar siyasa ba za ta iya da shugaban da shi ma yana fama da lafiyar kwakwalwarsa da kuma daidaiton siyasarsa.
Abun takaici a Nijeriya shi ne, ka bar jam’iyyarka a gwagwarmayar neman shugaban kasa, sannan ka zama dan takara na wata jam’iyya.