Ra’ayin ‘Yan Arewa A Kan Kafa Kasar Biyafara

Biyafara

Kwanakin baya ne kungiyar Dattawan Arewa ta bayyana amincewarta a kan bukatar kungiyar Iyamura ta IPOB na neman ballewa daga Nijeriya, a kan haka ne filinmu a yau ya nemi jin ra’ayin al’umma ko sun amince da shawarar kungiyar Dattawan Arewa na a bar su su kafa kasarsu kowa ya huta? Ga dai ra’ayoyin wasu ‘yan Nijeriya da filin ya tattauna da su.

 Hassern Mustapha

Ai IPOB sun nunawa duniya cewa su marasa kunyar karya ne kuma muma mun gane daman gwamnatin ta san yadda za ta yi maganinsu ta kyalesu. Sannan ina goyon bayan maganar dattawan arewa cewa kuma da zarar an fiddasu daga Nijeriya a tabbata sai sun yi Bisa za su shigo kuma duk abinda za a shigar musu da shi sai sun siya ninki 4 a kan yadda ‘yan Nijeriya za su siya.

 

Jamila Seyoji

To meye a ciki idan har hakan zai kawo zaman lafiya a yi mana, amma fa Ojukwu ma ya yi abin da yafi haka sai dai bai kai ga cimma nasara ba. Ita wannan kungiya ta IPOB sunayin haka ne domin tada fitina ga kuma shima Sunday Igboho mai fafutukar kafa kasar Yarbawa, abar su kawai su kafa kasar su.

 

Prof-Sufyan Adams Yakub

Ba na goyon bayan rabuwa a yanzu. Duk ni’imar da ba a same shi a lokacin da kai ke hade ba, baza a taba samun sa a lokacin da kai ya rabu ba.

Tsamar da ke tsakanin bangarorin nan guda biyu (Arewa da Kudu) a yanzu, a karkashin jagoranci daya, zai ninku ne a yayin da aka ce kowa na da na shi jagoranci.

Mafita kawai, su yi hakuri, sannan shugabanni su yi adalci. Idan har hakan ya ki kawo mafita, to babu mafitar da ta wuce a rabu. Domin wasu lokutan a cikin rabuwa ne a ke samun alheri, ba haduwa ba.

 

Adamu Yunusa Ibrahim

Suna na Comrade Adamu Yunusa Ibrahim.  Ni mazaunin Kano ne. A ra’ayina ina goyon bayan a bar ‘yan kungiyar aware ta IPOB su kafa kasarsu, tunda sun nuna ba sa son zama tare da mu. Mu ma mu kafa tamu da ta dace da addinin mu da al’adunmu.

 

Sameenu Reina Journalist Danbatta

Ina ganin hakan zai fi, a barsu duk inda za su suje tunda sun matsa suna son barin kasar kawai su ware Allah ya sa haka ne mafi alkhairi sannan kuma Allah ya dawwamar da zaman lafiya a kasar mu Nijeriya dama duniya baki daya.

 

Maryam Rabo

Gwamma a raban in har shi zai kawo karshen kashe kashen da ake yi ba gaira ba dalili, game sha’awar zaman kudu kuma sai ya nemi bisa.

 

Maidawa Sufyan Ibrahim

A fahimta ta, ita Nijeriya kasance da aka ce an kirkireta karkashin mulkin farar hula tun a shekarar 1960,  duba da yadda tsohon shugaban Amurka ya bayyana mecece Dimukradiyya. Duk da cewa ita Nijeriya tafi karkata a kan tsarin mulkin Amurka, ba kamar tsarin da suka kasance akai ba lokacin da aka bata ‘yanci.

Duk da haka, ganin kamun ludayin mulkin Nijeriyabai kawo canjin komai ba, hasalima wargaza kan jama’a ya yi duk a karkashin mulkin farar hula. Wanda mutane da dama suna ganin gwara mulkin soji da irin wannan mulkin da ake ciki.

Su ‘yan IPOB munane ne kamar kowa, tare da tunanin za su tsira idan suna samu ‘yancin kai, sun kasance mutane ne masu takaitaccen tunani wajen nuna fifiko ga wasu al’umma koma bayansu. Sun dauki tsawon lokacin suna irin wannan tabargazar ganin an basu kasarsu. Wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da dukiya mara adadi wanda kashi 75 na ababen da aka yi asararsu na ‘yan Arewa ne, amma duk da haka basu tunani gobensu ba.

 

Aysher Seyoji

Kwarai kuwa ina goyon bayansu 100/100,  duba da yadda al’amuran Nijeriya yake tafiyar hawainiyya ta dalilin haka, saboda kusan duk matsala da ake shiga a kasar nan kashi 50% zaka samu ta dalilin ‘yan kudu ne, imma ta addini ko ta al’barkatun kasa ko ta yare.

 

Ibrahim Hassan Baban Adila

Agani na kawai abarsu su kama gabansu, ma’ana su balle daga yankin kasar Nijeriya kowa ma ya huta daga mu ‘yan arewa har su ‘ya IPOB din.

 

Maryam Nuhu Turau

Ai kawai gwamnati ta amsa kiran ƴan kungiyar Dattawan Arewa, a yi wa ‘ƴan Aware yadda su ke so kwai a ware. Wace tsiya su ke tsinana mana in ba kashe ‘ƴan uwanmu da su ke yi ba?  Rashin kunyarsu ta yi yawa.

 

Mariya Jika

Gaskiya Ina goyon bayan a rabu din. Su tattara inasu-inasu su tafi din ba duk kokari irin nasu sun san in ba arewa din su ba komai ba ne domin nasha haduwa da ‘yan kudu da idan nace a rabu din yadda mutanen suke so za ki ji za su ce, ina ai za su kashe juna na ne a csn da tsafe tsafen banza

 

Bello Shazali Dambatta

A gaskiya ko kadan bana goyan bayan raba Nijeriya saboda wasu tsirarun mutane kawai za a ce a raba Nijeriya to gaskiya bana goyan baya ko kadan, Allah ya daukaka mana Nijeriya, amen summa amin.

 

Ibraheem Yunuz

Na tabbatar da cewa, su dattawan Arewan mutane ne masana don haka wannan shawarar tasu yana da muhimmanci, suna kuma hiwa arewa fatan alheri ne, don haka a raba kawai.

 

Zainab Danyaya

Ina ganin gara a raba din, gani suke su din wani abune amman idan aka raba ba tare da an yi tashin hankali ba sai aga sun gane kurensu muma ya Nijeriya mun huta da gunagunin da suke yi wadanda suke son zama da su sai su bisu, Allah ya zaunar mana da kasarmu lafiya.

Khadija Muhammad

Abin da Dattawan Arewa suka fada daidai ne saboda gani suke yi kamar sune kasar alhali Arewa ita ce Nijeriya saboda ta karbi duk wani baki daga kasar baki daya kuma suna zaune cikin jin dadi da kwaciyar hankali amma mu kuma sun hana mu sukuni a kasashen su saboda haka a basu abin da su ke so, ko yayanmu za su sami gurabe da suka mamaye a arewa mu kuma gani su za su shiga wahala.

 

Shamsi Umar Bakanike Danbatta

Hakan yana da kyau in har zai kawo mana zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan kasa tamu ta Nijeriya da fatan dai Allah (SWT) ya cigaba da bamu dauwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali ako da yaushe.

 

Exit mobile version