Yau dai na dauki alkalamina da takarda don in dan yi takaitaccen bayani akan abin da ke neman zame mana ruwan dare a tsakaninmu mu matasa yan arewa wanda kuma ya kasance yawancinmu duk musulmi ne yayan musulmi kuma.
Cacar bet9ja wadda a ke yi a halin yanzu ta kai ga har ta fara zame wa matasanmu dole, wanda a da kallon kwallo kawai muka sani amma yanzu bet9ja ya sa mun koma ‘yan caca da karfin tuwo, abin da muka sani a harkar wasan kwallo wanda turawa ne suka fara mu kuma muke kwaikwayonsu shi ne zaka dauki daya daga cikin kungiyoyin kwallon kafa dake buga babbar gasa a Turai sai ka dinga goyon bayan ta samu nasara a kan ‘yar uwar hamayyarta idan suna wasa
Amma yanzu abin ya wuce kawai goyon baya sai kaga mutum ya shiga shagon da ake cacar bet ya zura kudi masu yawa a kan cewa kungiyar da yake goyon baya ita za ta yi nasara, kaga kenan idan hakan bata yiwu ba a karshen wasan ya yi biyu babu, wani ma kudin da zai saka ba nasa ba ne ko kuma iya abin da yake gareshi kenan amma tunanin zai samu masu yawa idan ya saka a cacar zai sa ya zura kudin sa ba tare da tunanin idan aka yi rashin sa a babu wanda zai mayar masa da ko kwabo bayan haramcin caca a dddinin musulunci kuma akwai illa mai yawa ga duk wanda yake caca sabo da zai iya rasa duk abinda ya mallaka wajen neman ya dawo da abin da ya rasa.
Daga karshe ina jan kunnen masu wannan dabi’a da su tuna ko a al’adar bahaushe caca bata da kyau har ma wasu na ganin cewa dan caca barawo ne ko bai taba sata ba.
Kadan daga cikin illar cacar bet9ja shi ne rashin nutsuwa da duma rashin gaskiya inda akwai wani labarin wani mai suna Bala wanda wannan caca ta bet ta zame masa tamkar ibada inda ko wane lokaci yana shagon da ake gudanar da wannan mummunar sana’a idan kuma baya shagon to yana gida yana kitsa yadda idan ya samu kudi zai buga bet ta yadda zai samu nasarar cin makudan kudade, yana ta tunanin yadda zai kaucewa faduwa da rashin nasarar da ya dinga samun a duk lokacin da ya buga bet, shi ne sai ya tunkari wani abokinsa da ya taba cin 75,000 a wani wasa da ya buga domin ya tambaye shi shawarar yadda shima zai ci kudade.
Da ya tunkare shi da batun shawara sai wannan mutumin ya fada masa cewar ba haka kawai ake nasara a caca ba musamman ma ta bet9ja idan har yana son ya ci kudi masu yawa sai idan zai iya saka kudade masu yawa shima domin idan kana da kudade masu yawa sai ka saka su a kan wasan da zai iya faruwa cikin ruwan sanyi ba tare da ka sha wahala ba sai ka sa masa kudi masu yawa ta yadda idan hakan ta faru sai ka samu kudade masu yawa kaima a haka ya tafi yana shawara inda zai samu kudi masu yawa kamar 50,000 domin ya saka wa wani wasa da yake ganin kamar zai shiga cikin sauki, ana nan wata rana kawai sai mahaifiyarsa ta bashi kudi domin ya siyo mata buhun masara dana wake domin ita dama sana’ar ta kenan sayar da kayan abinci don haka ta bashi 25,000 na buhun wake sai 20,000 na buhun masara ta umarce shi da yayi sauri ya siyo sabo da kayan sun kare a wajen ta kuma bata son abokan huldar ta su zo nema ba tare da sun samu ba, shi kenan ya karbi kudi ya fito gida da niyyar zai je ya siyo mata abin da ta umarceshi ya siyo mata, yana cikin tafiya sai ya tuna to ai yau akwai wasan kwallon kafa da Chelsea za ta kara da kungiyar kwallon kafa ta Nottingham Forest wacce duka duka ma a wanna shekarar ta samu fitowa daga gasar yan dagaji ta kasar ingila zuwa babbar gasar firimiya lig, kawai sai ya tuna da kudin da ke wurinsa wanda mahaifiyarsa ta aike shi da su sai ya ga idan yasa su a wannan wasan a matsayin kungiyar kwallon kafa ta chelsea ta samu nasara a kan abokiyar karawarta zai samu nasa kudin daga cikin na mahaifiyarsa kawai sai ya canza hanya ya tunkari shagon da ake buga bet da zuwa sai ya isko mutane da yawa suna ta buga wasannin kala kala kowa da irin abin da ya ke bukatar a buga masa aiko ya samu guri ya tsaya sai da layi ya zo gunsa mai buga wasa ya tambaye shi what do you want to play (me za’a buga maka) ai kawai gogan naka ya zaro 45,000 daga cikin aljihun rigarsa ya mika wa mai shago ya ce buga min Chelsea winning, mai shago ya karbi kudi ya kirga 45,000 cif sai ya buga masa ya mika masa takarda shi kuma ya wuce bai tsaya ko ina ba sai gidan kallon kwallo ya samu an fara wasan da minti 16 har ma chelsea ta ci kwallo daya ta hannun dan wasan ta Rahem Sterling aiko da ganin haka sai ya zaro ticket da aka bashi daga cikin aljihun rigarsa ya duba yaga idan har wasan ya tashi a haka zai samu 65,040 wato ya samu ribar 20,040 idan ya cire kudin da aka aikeshi ya sayo buhun masara da na wake, ganin haka ke da wuya sai ya roki mai tsaron gidan kwallo da ya bari ya shiga amma bashi da kudi amma ya mishi alkawarin idan har aka tashi wasan zai tafi gida ya dauko masa naira 300 a maimakon 100 da ake karba a matsayin dudin kallon kwallo a haka sai mai tsaron gidan kwallon ya bari ya shiga da shigarsa ya samu wuri ya zauna ya cigaba da kallon yadda wasa ke gudana, bayan minti 45 alkalin wasa ya bushe wasa domin tafiya hutun rabin lokaci, bayan an dawo Bala ya cigaba da kallon wasa yana ta ihu yana ana yi muna jin dadi!! ana nan wasa ya yi zafi sai kawai Bala yaga dan wasan forest Serge Aurier ya zura ball a ragar Chelsea wato ya farke kwallon da Chelsea ta jefa kenan aiko Bala ya shiga damuwa fuska ta canza gaba daya ya dawo bashi da sukuni ko kadan.
Yana cikin wannan yanayi sai wayarshi ta dauki ringing ya duba yaga lambar mahaifiyarsa ce take kiranshi aiko ya fara shawarar ya dauki wayar ko kuma a’a, haka sai ya daure ya dauka, daukarsa keda wuya sai mamarshi ta hau shi da fada tana cewa ya akayi har yanzu bai dawo gida daga sakon da ta aikeshi, Bala ya kada baki ya ce wallahi wani abu ya bata mini lokaci a kan hanyata ta zuwa kasuwa amma dai ina nan zuwa bada jimawa ba, Bala ya kashe waya bayan mahaifiyarsa ta fada masa cewa ya yi maza ya dawo in ko ba haka ba ta bata mishi rayuwa, bayan mintuna 90 ana fafata wasa tsakanin Chelsea da Forrest sai alkalin wasa ya kara mintuna biyar domin tashi daga wasan anan fa Bala ya rasa mi ke mashi dadi a duniya tun da in har chelsea bata samu nasara ba a wannan wasan hakan na nufin ya yi asarar naira 45,000 da aka aike shi kasuwa dasu, a minti na 95 alkalin wasa ya bushe wasa inda aka tashi 1-1.
Bala ya tashi ya fita waje tare da sauran jama’a, a hanyar sa ta fita mai tsaron gidan kwallo ya tuna masa da alkawarin da ya dauka na kawo masa 300 idan an tashi, a haka sai ya fita yana jimamin kudin mahaifiyarsa da suka shige a caca, Bala bai zame ko ina ba sai ya wuce inda ake saida wayoyi ya sayar da wayarsa kirar Tecno a kan kudi naira 2,500 aka bashi kudin sa ya tafi tun daga ranar Bala bai sake komawa gida ba sai bayan kwana uku ya koma ya nemi yafiyar mahaifiyarsa kuma ya fada mata abin da ya auku a ranar da ta aike shi kasuwa ya sayo mata buhun wake dana na masara abinka da uwa da da ta yafe masa kuma tayi masa gargadi a kan ya daina yin caca idan har yana son ya yi albarka a rayuwa, tun daga ranar Bala ya koma mutumin kirki ya bar wannan dabi’a ta caca ya koma shagon koyon dinki domin cigaba da koyon aiki a wurin mai gidansa.
wannan labara yana nuna mana yadda wannan mummunar sana’a ta bet9ja ke zama sanadiyar lalacewar matasan mu har ta kai ga sun fara kasha duk abin da yazo hannun su ba tare da tunanin ko nasu ne ko kuma ba nasu bane, a wani lokaci ma wasu kan yi sata domin samun kddin buga bet sabo da haka muke fatan matasan mu musamman masu kallon kwallo a kan su tsaya a matsayin sun a masu sha’awar harkan kwallo ba tare da sun zama ‘yan caca ba kuma idan har ka riga da ka fara wannan dabi’an akwai hanyoyi da ake bi domin bari, na farko ka kaurace wa zuwa duk wani wuri da ake buga bet domin idan har kana zuwa ba za ka taba bari ba sabo da ganin wani yana yi zai iya janyo maka ra’ayi kaima ka yi, sannan idan da wayarka ta tafi da gidanka kakeyi sai ka goge akawun naka na bet wato deactibating sannan ka dauka a ranka cewa caca ko a addinin musulunci haramunce babba kuma wata hanya ce da ke zurare maka kudi ba tare da ka amfana ba.
Na gode.
Rabilu Sanusi 09018385364
[email protected]