Tun daga ranar da aka wayi gari jaridar LEADERSHIP A YAU ta fara fitowa a kullum masu karanta jardar a lokacin da take fitowa a ranar Juma’a suka fara tsokaci daban-daban, kuma sun bayyana ra’ayoyinsu ne a zantawar da suka yi da wakilinmu da ke Zariya.
- Alhaji Sale Moriki
Wani masanin harkokin tsaro, shugaban al’umma, Mai Unguwar Layin Zamfarawa, kuma uba a kungiyar ‘yan kasuwar sayar da takin zamani ya bayyana cewa in har ana maganar jaridar harshen Hausa ne, ya fara karanta jaridar ne GASKIYA TA FI KWABO da aka fara bugata a shekara r ta 1939.
Alhaji Moriki ya ce tun daga waccan shekarar, ya rungumi jaridun Hausa da hannu bibiyu, kuma ya ce yana yin tsokaci ga al’amura da dama da suka shafi ci gaban Nijeriya.Ya kara da cewar, duk mai karanta jaridun Hausa, ya san sunansa ba bakon suna ba ne a shafukan jaridun.
Amma game da fitowar LEADRSHIP A YAU a kullum, Alhaji Sale Moriki ya ce duk wanda ya kalli jardar ya san ta yi fitowar muricin kan dutse, na yadda ta tsara jaridar da kuma yadda ake kokarin ganin an rubuta abubuwan da masu karatun jaridar suke so.
Ya kuma tabbatar da cewar yadda al’ummar da suke karanta jaridar suka rungumi jaridar da hannu bibiyu, to wajibi ne masu dauko rahotanni da ake sawa a jaridar su kara tashi tsaye, na ganin sun ba marada kunya, da suke ganin sun dauko aiki mai yawa.
Alhaji Sale Moriki ya kammala da cewar, zai kyau jaridar ta fito da wani shafi da masu karanta jaridar za su rika rubuta ra’ayoyinsu da ya shafi jaridar ko kuma wasu al’amurra da suka shafi ci gaban al’umma na ciki da wajen Nijeriya.
- Malam Bawa Mai Sayar Da Jarida
A lokacin da wakilinmu ya ziyarci PZ, cibiyar sayar da jaridu ta
Zariya ya yi tozali da Malam Bawa, wanda duk mai sayen jarida ko jaridu a PZ ya san sunan, ba bakon suna ba ne fiye da shekaru talatin da suka gabata.
Malam Bawa ya ce, ranar da ya ji labarin LEADERSHIP A YAU za ta fara fitowa a kullum, sai ya ce sun dauki matakan share wa masu karatun jaridun Hausa hawaye, domin a halin yanzu, ya fi kowa sanin bukatar da al’umma ke yi na jaridun Hausa a Zariya.
Sai dai ya ce, abu biyu yake son shugabannin jardar LEADERSHIP A YAU su kiyaye, abu biyun su ne, a sa ido a ga ana kawo jaridar a kan lokaci. Na biyu, a kara yawan jaridar da ake kawowa Zariya. Kamar yadda ya ce jaridun da ake kawowa ba sa isan kashi biyu a cikin goma na masu bukatar karantata.
- Malam Sani Aliyu Basawa
Shi kuma wannan matashi ne da ya shafe fiye da shekara goma yana sayar da jaidu a PZ Sabon Garin Zariya. Ya ce babbar shawarar da zai bayar, a kula da kawo jaridar a kan lokaci, kuma a kara yawan jaridar da ake turowa Zariya. Kamar yadda ya ce, su da suke sayar da jardu, sun fi kowa sanin yadda al’umma ke son jardar LEADERSHIP A YAU.
Daga nan sai Malam Sani Basawa ya jinjina wa ma’aikata da mahukuntan wannan jarida na wannan babban aiki da suka dora wa kansu da nufin share wa masu son karanta jaridun Hausa hawaye.