Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RA'AYI

Ra’ayoyin Masu Karatu: Wa Zai Gaji Buhari?

by Tayo Adelaja
September 24, 2017
in RA'AYI, WASIKU
6 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Kamar yadda mu ka yi mu ku alkawari a makon jiya cewa, LEADERSHIP A YAU (LAHADI) za ta ware shafi guda, domin ku bayyana ra’ayoyinku kan Babban Labari da mu ka kawo mu ku a makon jiya, Editanmu na Yanar Gizo, JAMILU ADAMU, ya tattaro ra’ayoyin da ku ka bayyana a shafinmu na FaceBook, Leadership A Yau. Mun ba ku wannan dama ne, domin kara dankon zumunci a tsakaninmu da kuma ba ku damar ’yancin fadar albarkacin baki. A sha karatu lafiya:

ABDUL BAKO: In sha Allah, Allah zai bawa Baba Buhari lafiya da tsawon rai mai amfani, kuma sai ya yi shekara takwas yana Mulki Nijeriya cikin yaddar Allah, Muna Addu’a Allah ya kara masa lafiya, Allah ya kare shi daga sharrin makiya nafili da na doye Amin.

samndaads

 

RUKAYYA ADO: In sha Allahu Kwankwaso ne zai zama shugaban kasa, saboda gaskiyar magana Buhari ba shi da lafiya, ga tsufa, sannan a hakan ma abubuwa ba sa tafi ya yadda ya kamata saboda kullum ba ya nan, muna rokon Allah ya bawa buhari lafiya, shi kuma Kwankwaso Allah ya bashi ikon rike Nijeriya.

SANUSI M JIBO: To ni dai a nawa ra’ayin Osinbajo ya kamata ya hau wannan kujera, abinda ya sa na ce haka duk gwamnonin Nijeriya barayi sun fi yawa. To amma sai idan babu makawa baba Buhari ba zai iya tsayawa ba a zaben 2019 ba, saboda rashin lafiyar da ALLAH ya jarrabe shi da ita, bayan haka muna rokon ALLAH ya saka muna daga cutarwar da barayin Nijeriya suke yi, a karshe muna rokon ALLAH ya ba baba Buhari lafiya Allahumma Amin.

 

MARYAM HARUNA: To Allah shi ya san daidai damu wandazaimana adalci amma maijiya ta yi ballantana yau insha Allahu sai baba Buhari allah kakaramasa lafiya nisan kwana kuma Allah ka bashi juriyar rike amanar ‘yan Nijeriya amma duk sauran? Akwai alamar tambaya a kansu Allah ka taimaki mai tausayin talakawanka.

 

MUKTARI ALHAJI: Allah ka yi muna jagora ka bawa Kwankwaso Shugaban kasa a Nigeria ameen summa amen.

 

MOHAMMED ABDUSSALAM: Dukkansu su yi hakuri sai 2024 da ikon Allah domin ai BABA BUHARIN muna tare da shi har wancan lokacin da izinin Allah amin.

ALIYU MU’AZU YELWA: Ai wani kaya sai amale baba Buhari kawai mu shi muke so Allah ya kara lafiya G.M.B Amin.

 

SHAMSU LAWALI: Idan Allah ya yarda Buhari zai sake tsayawa, kuma shi zai lashe zaben 2019.

 

AUWAL ABUBAKAR: Mu dai shi muke so baba Buhari koma in Allah ya yarda shi ne Dan takaran APC 2019.

 

MAHMUD ABUBAKAR KOFA:  Ai wannan a bayyane yake magajinsa ba kowa ba ne kamar ya ce shi ma shugaban ya fada da bakinsa, idan ba kai ba wa kake gani Kwankwaso.

 

MUKTAR MUHAMMAD JAMA’A: Allah ka zaba mana wanda ke son mu ba wanda muke so ba kuma mai tausayinmu wanda zai damu da damuwarmu.

 

MUHAMMAD JAMEEL: Idan sha Allah Dan Musa ne zai gaje shi da yardar Allah a 2019 Dan Musa mai Allah ya ida nufi Allahumma Ameen.

 

AL-KASIM ADAMU SIYI:  Sai Dan Musa mai kishin kasa, idan ba shi ba gara ‘yan kudu da wadannan azzalumai daga mai bakin fika, sai dan giya sai dan Boko Haram sai barawo, sai mushirkai.

 

MADAKI LAGOS: Allah Ya yi mana zabin wanda ya fi zama alhairi a garemu, ba wai wanda muka fi so ba; kuma muna wahalar da kanmu a kansu ba su san muna yi ba.

 

ABDULAZEEZ MASHI: To mu dai Allah ne gatanmu, in ya bawa Buhari lafiya, fatanmu kenan to ya fiye mana duk wadannan.

 

MOHAMMED BUKAR: Ciwon hauka ne dangane da mulkin kasata. Kuma da dama daga cikin masu hasashen in sha Allahu sai dai Allah ya yi hukuncinsa ga wanda ya so. Amma mu kam musamman irina, sai Baba Buhari in sha Allah.

 

NAZEEFI SANI:  Ka ji wani kuma wai Sule Lamido, to wa ya san shi, kuma wa ya sani. Mu kam muna bayan mara tsoro……….. Rabi’u Musa.

 

MUSTAPHA ATTAHIRU FAGGE FAGGE:  Duk wanda ya daga hannu a cikinsu ya ce bai taba satar kudin Niijeriya ba, to shi zamu zaba

 

MARYAM MUHAMMAD ASSALAFIYYAH: Ni a nawa ra’ayin idan ba Buhari ba to Osibanjo ko Malam Nasiru ko Tinibu. Su ne nake ganin suna da sauran alamar tausayi.

 

SAHAL MOHAMMED:  Duk yamutsi ne babu wanda ya cancanta a cikin su kar Allah ya dora mana daya a cikinsu shir me kawai, sai baba Buhari 2019.

 

MUSTAPHA MUSA MUHAMMAD: Gaskiya ni ma ina san Baba Buhari amma idan har ya nuna cewa ba zai yi takara ba saboda tsufa da kuma larurar dake damunsa tofa Kwankwasiyya ne gwanina na 2019.

 

DALHA A DANJUMA: Allah ka bawa babanmu na Daura lafiya, kuma ya kashe makiyansa da mahassada Ameen. Ya Allah albarkacin Nana Aisha ka ba Baba Buhari lafiya sannan ka ba aba Kwankwaso shugaban kasa.

 

ZAKARI HARUNA: Dankwambo muke so yanzu, matashi ya kamata ya karbi Baba Buhari.

 

MANSIR ABU SURAIYA:  Ku ke nan ba ku da abin cewa sai maganan tsofaffin nan, idan Allah ya yarda sun yi sun gama in sha Allah ba wani tsohon da zai kara cin koda kansila a Nijeriya.

 

YUSUF RABILU BANGO: To sun gama koshi za su zo su raba fastoci, talakan Nijeriya mu yi addu’a Musulmi Allah ya sa mu cika da imani amin.

 

GHALI BELLO: Sardaunan Kano

 

NASURU SHEHU: Allah ya karawa mai son talaka lafiya shi ne baba Buhari amin, muna tare dashi.

 

SALISU LAWAN SALHAB: Allah ya bawa mai rabo sa’a, amma ra’ayina Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso Tsohon Gwamnan Kano saboda shi ma yana da kishin talaka.

 

SHEHU MALAMI ALKAMMAWA: Kwankwaso

 

BABAN GAMBO A AHMAD:  Baba ka yi ta yi har 2019 idan ka hada mu talakawa zamu fito kwammu da kwarkwatarmu mu kira a sake fasalin kundin tsarin mulki, ka yi ta yi Baba Allah na tare da kai dan marayan zaki.

 

MUBARAK ABDULLAHI: Babu adalin shugaba kaf Nijeriya, da ma Yar‘adua ne kuma ba ya da wadannan duk mugwaye ne.

 

SULAIMAN ALIYU:  Ai gara Osibanjo da sauran wadannan gayyar na ayyan.

 

ZAHARADDINI ABDULLAHI: Ai wallahi gwanda Osibanjo sau miliyan daya duk da ba Musulmi ba ne dan dukan su agwagi ne.

 

AUWALU YARO:  Shi zai gaji kansa. Ina wani ba shi ba, ka yi taka ka yi ta raggo. PMB.

 

BASHIR MUHAMMAJA GWAMMAJA: Shekarau.

 

HARUNA SHEHU ABUBAKAR:  Mallam Nasir el-Rufa’i.

 

AHMED ABBAKAR: Talban Gombe.

 

YAKUBU IDRIS ABUBAKAR TSOHO:  Allah dai ya yi mana tsari da mulkin Buhari.

 

MUSTAPHA AHMAD ABUBAKAR:  Kwankwaso 2019 shi muke fata.

 

NAZEER ABBA DUKAWA: Malam Ibrahim Shekarau muke Fata In sha Allah

 

SAEED PELLA: Sai Baba Atiku kawai.

 

MUHAMMAD B Z DAMAZI:  Cuta ba mutuwa ba sai baba Buhari 2019 in sha Allah.

 

GARBA MUSA:  Ai 2019: Sai baba Buhari don haka su yi hakuri.

 

AMINU MAI TSADA: Sai Buhari da Malam Nasiru.

 

BALANCY ZANGON DAKATA: Sai Kwankwaso.

 

DAUDA KWAJI: Farfesa Yemi Osibanjo.

 

MAHMUD MUHAMMAD KALLI: Daga Buhari, Sai Buhari.

 

ZAINAB YAHAYA:  Kwankwaso gugar karfe.

 

JAMIL ISAH:  Ga mai kishin kasa Dan Musa mai takalmin karfe Kwankwasiyya akida.

ABBASS AMIINUU: Ai bayan Buhari sai Dankwambo, sai Talban Gombe Sarkin aiki.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

“Rashin Gaskiya Ke Kawo Cikas A Kasuwanci”

Next Post

Cancanta Ta Sa Mu Ka Nada Fati Kulani Jakadiyar Pantami – Hakimi

RelatedPosts

Sabuwar Shekara

Wata Mahanga Daga Jawabin Buhari Na Sabuwar Shekara

by Muhammad
2 weeks ago
0

Daga Gidado Ibrahim, Jigo a tsarin shugabanci na Dimokradiyya shi...

Yadda Cin Zarafi Ke Neman Zama Dabi’ar Wasu ‘Ya’yan Jam’iyyar APC Ta Jihar Kano

Yadda Cin Zarafi Ke Neman Zama Dabi’ar Wasu ‘Ya’yan Jam’iyyar APC Ta Jihar Kano

by Daurawa Daurawa
2 weeks ago
0

Daga Usman Suleiman Sarki Mulkin dimokaradiyya tsari ne da ya...

Gwamna Buni

Gwamna Buni: Ina Aka Fito Kuma Ina Aka Nufa? 

by Sulaiman Ibrahim
3 weeks ago
0

An bayyana cewa duk da yanayin 2020, matsayin shekara wadda...

Next Post

Cancanta Ta Sa Mu Ka Nada Fati Kulani Jakadiyar Pantami – Hakimi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version