A wannan makon mun ji ra’ayoyinku ne a kan dambarwar siyasar data turnuke a Jihar Adamawa. Inda ta kai ga an dakatar da kidayar kuri’u aka kuma dakatar da Shugaban Hukumar Zabe na Jihar sakamakon sanar da cewa Aisha Binani ce ta lashe zaben gwamna na Jihar tun kafin a kammala tattara alkalumman zaben. Ga dai ra’ayoyin maku.
Muhammad Dahuru Tanko
Ai rabon kwado baya hawa sama
Engr Abdullahi Musbahu Dambatta
Allah dai ya kyauta
Ali Abdu
Hahaha 2b ba wasa ba
Ni dai ra’ayina shi ne yakamata hukumar zabe ta kasa ta yi adalci mu kuma talakawa mu kwantar da hankalimu saboda tayar da hankali ba shi ne zai sa abawa wanda mu ke so ba yakamata mu kaucewa duk wani abinda zai tayar da hankalin al’umma mu ci gaba da addu’ar Allah ya zaba mana mafi alkairi su kuma wanda suka bayyana wanna zabe yakamata a dau tsatsauran mataki a kansu saboda na gaba.
Mahdee Bashir
Gaskiya Ina tunanin ‘tension’ ne ya yi masa yawa, kuma dai an jero sau biyu macen ce a gaba, amma sarakuna da masu fada aji ba sa son ayi hakan duk da musulunci ma ya kalubalanci shugabancin Mata amma fa Nijeriya ba musuluncin ake yi ba
Sameenu Dahiru Abdullahee Dambatta
Ya dai kamata a yi adalci, a bawa mai gaskiya nasarar sa kada a nuna masa Nijeriya
Hadiza Bello
Yakamata a tabbatar da hukunta duk wanda ke da hannu a sanar da sakamakon zaben da bai inganta ba, ta haka zai zama darasi da ‘yan baya, na gode kwarai da gaske, Allah ya zaunar da kasar mu lafiya.
Ahmad Dan Maryam
Ra’ayina shi ne a ba duk wanda aka tabbatar da ya yi nasara, nasararsa, bai kamata a danne wa wani hakkinsa ba.
Barista Adam
Irin wannan dambarwar ke kawo wat sarin dimokradiyya cikas, ya kamata al’umma su farka
Ra’ayin Sheriff Almuhajir A Kan Bukatar Samar Da Dokar Wa’azi
Rashin dokar wa’azi da fadakarwa a kasar nan shi ya jawo mana musibar Boko Haram, har aka samu wasu mutane suke amfani da sunan addini, su karanta Kurani da hadisai kuma su kafa hujja da su sannan su afkawa mutane su kashe.
Daga farko sun fara da kashe jamian tsaro, suka koma kashe wadanda ba Musulmi ba, suka koma kashe Mallaman tsangaya da sunan bokaye, har suka koma kashe na su Malaman. Daga baya suka afka gari suna kashe mai uwa da wabi. Kai daga karshe suka koma suna kashe kan su da kan su, har suka koma dasa bomb a jikin su suna mutuwa.
Wannan abu ya fara ne tun 2009, amma abun mamaki yanzu muna 2023 shekaru goma sha hudu, amma har yanzu shugannin kasar nan ba su ga ya dace su kwaikwayi kasashe irin Saudiyya, Egypt, Morocco da sauran kasahen duniya da su ke da dokar wa’azi ba.
Anya hakan ya dace kenan?