A wannan makon mun kawo ra’ayoyinku ne a kan nasarorin da jami’an tsaro suka samu na fatattakar ‘yan ta’adda a yankin Abuja tun bayan umarnin da Shugaba Buhari ya bayar kwanakin baya, bayan da aka Kai wa rundunar da ke tsaronsa hari.
Omar Naseer Imam:
Masha Allah, Muna taya su da addu’a sosai kuma muna fatan wannan nasarar ya game Nijeriya gaba daya kananan jami’an tsaro suna kokari sosai sun bada ransu da duk wani farin cikinsu muna masu fatan alkhairi a koda yaushe.
- Salman Rushdie: Wanda Ya Yi Batanci Ga Annabi Na Cikin Mawuyacin Hali Bayan Kai Masa Hari
- Obasanjo Ya Roki Marayun Borno Su Yafe Wa ‘Yan Ta’addar Da Suka Kashe Iyayensu
Sulaiman Muhammad:
To aikuwa har yandu akwai matsala saboda ba a bin su inda suke zaune a cikin dajin kamar yadda suke kaiwa jama’a hari dare da rana suma haka ya kamata a yi musu da tuntuni an gama da wannan matsalar.
It’z Sam Dambatta:
Babu abinda za mu ce sai dai godiya ga Allah (SWT) bisa wannan nasara da aka samu, Sannan muna kara jinjina ga jami’an tsaro bisa wannan aiki da sukai dama munsan za su iya sai dai idan ba a sa su ba. Sannan muna kara tawassali da sunayen Allah na Alhayyu Alkayyum da ya kara inganta mana zaman lafiya da tsaro a kasarmu baki daya.
Umar Bello Ubd:
Abin a yaba musu ne amma mu dama laifinsu muke gani saboda an basu kayan aiki kamar mutoci na shiga daji da bindigogi da nauran gano inda suke.
It’z Jameel Moh’d:
Allah sarki kasata Nijeriya gaskiya muna cikin wani hali Allah ya kawo mana dauki cikin sauki ana kashe bayin Allah wanda ba su ji basu gani ba, ‘yan ta,adda suna daji daina kashe bayin Allah ashe ‘yan ta’adda ne saboda kowa ya sani cewa inda gaske suke yi sun san inda suke suje a ranar daya su gama da su.
Muhd Basheer Sa’ad:
Alhamdulillah Masha Allah!, wannan umarni da aka bawa jami’ai na fatattakar ‘yan ta’adda ya yi amfani sosai kuma Allah ya basu nasara, da ace gwamnati za ta basu dama kamar yadda ta basu a yanzun da to shakka babu za a samu nasara. Gwamnati bata damu da talakawa ba shi ne magana kawai.
Adamu Yunusa Ibrahim:
Tabbas abin a yaba wa hukumomin tsaro ne, domin sun kusa yin sake. Da a ce tun farko ana iya magance matsalar da ba za ta kai girman haka ba. Kowa ya ga yadda Gwamnati ke tura babban kason kasafin kudi a duk shekara ta fannin tsaro, amma sam kwalliya ba ta biyan kudin sabulu. Don haka, matukar ana so a kawo karshen matsalolin tsaro a kasa baki daya, wajibi ne a fito da shirin ba sani ba sabo, kuma a yi tsayuwa irin ta masu daka wajen ganin an kakkabe bata garin da ke cikin al’umma.
Hukumar tsaro ta farin kaya DSS da hukumar tsaro ta sirri SSS Da hukumar leken asiri ta kasa, da hukumar ‘yansanda da Sojojin kasa da na sama da na ruwa da hukumar Cibil Defence, da hukumar hana fasa kwauri ta kasa Customs da hukumar kula da shige da fice ta kasa Immigration, da duk wata hukuma da tsaron kasa ya rataya a wuyansu, ya zama wajibi su kara kaimi wajen kiyaye nauyin da ya rataya a wuyansu nan tsaron rayuka da dukiyoyin jama’ar kasa.
Domin ba su da wata kasa sai Nijeriya, idan Nijeriya ta durkushe su ma sun durkushe.
A karshe ina sake jinjina wa jami’an tsaron da su ke hana idanuwansu bacci domin gudanar da ayyukan su na yau da kullum har suka kakkabe bata gari daga yankin Abuja. Muna fata, za su kara kaimi wajen fadada Ayyukan su, a jihohin Sakkwato da Zamfara da Katsina da Kaduna.
Allah ya taimaki kauyukanmu da mazabunmu da kananan hukumominmu Gundumarmu da Jiharmu da Arewacin Nijeriya da Kasa baki daya. Amin.
Comrade Adamu Yunusa Ibrahim, Malami a Cibiyar Nazarin Hausa, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriya.
Nuruddeen Muhammad Funtua:
A gaskiya wannan nasara muna matukar godiya ga Allah (S.W.A.) muna addu’a a gare su bisa wannan namijin kokari da suke yi Allah ya cigaba da basu nasara ya kuma kiyaye manasu a duk inda suke Allah ya kawo mana karshen wannan tashe-tashen hankula aduk fadin Nijeriya baki daya Ameen ya Hayyul kayum.
Yusuf Muhammad Jalingo:
Mude muna kara kalubalantan gwamnati da masu ruwa da tsaki wajen yadda ‘yan jarida suke kokarin nemo labarai wanda har za su iya kutsawa jeji su bankado inda ‘yan ta’adda suke su dauko labarai to haka muke so jami’an tsaro suma suyi haka ko fiye da haka wajen kaiwa ‘yan ta’adda hari da kuma dakile duk wani hari nasu, sai dai jami’an tsaro suna kokari, Allah ya kara lalata shirin masu sharri, Amiin.