Connect with us

LABARAI

Ramadan: Malamin Addini Ya Yi Kira Ga Masu Hannu Da Shuni Su Taimaka Wa Marayu Da Marasa Galihu

Published

on

A daidai lokacin da ake kokarin fara gudanar da Ibadar Azumin watan Ramadan mai Alfarma, wanda al’umman musulmai ke azumta bisa umurnin Allah Madaukaki.

An kirayi masu hannu da shuni a kowani lokaci suke kokarin taimaka wa marayu da marasa galihu a cikin al’umma a cikin wannan wata ta Ramadan da ke gabanmu.

Wani malamin addini da ke Bauchi Sheikh Ahmad Tijjani Guruntun, shine ya yi wannan kiran a lokacin gabatar da jawabi kan watan Ramadan wanda ya gudana a ranar Asabar a masalaciin S-19 Mosque da ke Bauchi.

Sheikh Tijjani Guruntun ya nuna buqatar da ake akwai wajen ganin mutane sun yi amfani da lokacin wajen faranta wa marasa shi rai, haka kuma ya kirayi jama’an musalmai da suke kokarin sadaukar da abinci, da sauran kayyakin bukatuwa ga jama’an da basu da hali a tsakanin al’umma domin samun lada daga wajen Ubangiji Allah.

Yana mai bayanin cewar sakamakon lada da Allah ke baiwa dukkanin wani wanda ya yi aikin alkairi a watan ramada, Allah na ninka wa kowani mutum ladar ne, don haka ne ya nemi jama’a su yi tururuwan samun wannan nasarar da ke tafe a cikin watan Ramadana.

Malamin yana mai bayanin cewar da zarar watar ta wuce shi kenan kuma, ya bayyana cewar ba lallai ne mutum ya samu zarafin maimaita wata Ramadan din, don haka ne ya hori jama’a su yi aiyukan alkairi a watan domin dacewa.

Sheikh Guruntun ya bayyana cewar a daidai watan da jama’a suke gudanar da Azumi, da akwai gayar buqatar kowani mai azumi yake gudanar da halaye na kwarai gami da kauce wa gudanar da munanan dabi’u a cikin watan na ramadan, kana ya kuma hori musulmai su shagalta da ibada, karantu Kur’ani da sauran halaye na kwarai domin dacewa da dukkanin ababen da ake iya samu a cikin watan na Ramadan.

Ya yi fatan jama’a su gudanar da Ibadarsu karbabbiya, yana kuma mai cewa kowani mutum ya tsarkake zuciyarsa domin shiga cikin wata mai alfarma.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: