Connect with us

RAHOTANNI

Ranar Bayar Da Jini: Kaso 10% Kacal Na ‘YAn Nijeriya Ke Bayar Wa Kyauta –Gwamnati

Published

on

ayinda ake ranar bikin bada taimakon jin ta duniya, an yi kira ga ‘yan Nijeriya dasu bada taimkon jini. Gwamnatin Nijeriya
Gwamnatin Nijeriya ta bayayna cewar yayin da maza ya dace su bada gudunmawar jini, ko wanne watanni hudu, su kuma mata ya kamata su yi hakan, a ko wanne watanni uku, saboda hakan zai sa, a samu yawan jinin da ak so, wanda ya kai unit milyan 1. dubu dari takwas (1.8 milyan) ko wacce shekara. Ministan lafiya Isacc Adewale shi ya bayyana haka ranar bada taimakon jini ta duniya, ta shekarar 2018,a lokacin da yake ganawa da manema labarai a A buja ranar Alhamis,ya nuna rashin jin dadin shi, ga wadanda ke zuwa su bada gudunmawar jini , bai taka kara ya karya ba, a Nijeriya.
Mr Adewole ya bada alkalumman da suka nuna cewar kashi goma ne cikin 100, na ‘yan Nijeriya suke bada gudunmawar jini,domin amincewar kan su ba tare da sai an basu wani abu ba, sai kuma kashi 60, su suna badawa ne saboda kudi, yayin da su kuma sauran kashi 30 kuma su suna ba ‘yan uwansu ne kawai, wadanda suke da bukata. Donhaka shi Ministan yayi kira ne da mutane su batar da taimakon jini, ba wai saboda kudi ba kawai.
‘’Shi bada jini akai akai yana da na shi muhimmancin, da farko dai akwai wani binciken da ya nuna cewar, mutane wadanda suke bayar da jini kyauta,su suna da damar cikin ikon Allah su yi tsawon rai, kamar daii yadda shi Ministan ya bayyana’’. An dai ware ko wacce ranar 14 ga watan Yuni kasashen duniya suna bikin ranar bada taimakon jini ta duniyata (World Blood Donor Day WBDD). Shi dai wannan biki an fara yin shi ne cikin shekarar 2004, saboda a samu damar wayar da kan jama’a, akan da akwai bukata ta a bayar da taimakon jini mai kyau, da kuma kayayyakin da suka kunshi jini, a kuma godewa masu bada taimakon jini, saboda sun bada ne domin su samu ceton rayukan muatane. Kamar dai yadda Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana cewar, domin tabbatar da anasamar da jini mai kyau nagartacce, isasshe, ana da bukatar da a, arika yin hakan ba tare da sai an tilasatawa mutune ba , kuma kyauta wato ta bada gudunmawar jinin. Amma kuma duk da hakan al’amarin daya shafi jini, yana fuskantar matsaloli, da suke kawo cikas wajen samar da isasshen jini, da kuma tabbatar da nagartar shi.
Nijeriya dai ta kasance a karkashi kasashe wadanda basu da isasshen jini, wanda ake ajiyewa, amma kuma yayin da ba a samun jinilokacin da ake bukatar shi, ga wadanda basu da lafiya. Wannan shi yasa su asibitoci sun fi dogaro ga ‘yanuwan marasa lafiya su bayar da jini, ko kuma su biya wadanda suk ayardea a debi nasu, inda ake ba mutane kudi saboda su bada jinin su a taimakawa marasa lafiya.
Kididdigar majalisar dinkin duniya ta nuna cewar, ana samun jinin da ake badawa taimako, ana samun kusa da miyan 112 da ake samu daga fadin duniya, wani abu kuma fiye da rabin wannan jini ana samun shi ne daga kasashe wadanda suke da kudaden shiga masu yawa, wannan ya nuna ke nan kamar kashi 19 na yawan jama’ar duniya. Kasashe 57 kadai suka samun jinin da suke bukata wanda ya kai kashi 100, daga kungiyoyi masu zaman kansu, wand aba kudi ake badawa ba. Shi kuma Henry Ewononu wani masani a bangaren daya shafi kiwon lafiya cewa yayi, da akwai bukatar a wayar da kan ‘yan Nijeriya, akan muhimmancin bada taimakon jini, ba tare da an matsa wa wanda ya bada din ba.
‘’Akwai bukatar a samu cimma wani mizani wanda ake son Nijeriya ta samu kaiwa ga, saboda bamu bada gudunmawar jini hakanan kyauta,kashi 10 ne na ’yan Nijeriya suke bada jin kyauta.
‘’Idan mutum ya bada taimakon jini za a gwada shi akan cututtukan da suka shafi HIB, Hepatitis, A,B,C, Syphilis, da daisauran wasu cututtuka. Wannan yana taimakawa wanda ya bada taimakon jinin ya san irinhalin da yake ciki. ‘’Idana ka gano baka da duk wadannan cututtukan, akwai wani abinda yake bada kwarin guiwa, da ka ci gaba da rayuwa irin wadda kake yi, ya kuma guji yin rayuwar da bata dace ba.
‘’Bugui da kari kuma rayuwar red blood cell a jikin mutum ita ce kwana 120, amma kuma idan mutum ya bada taimakon jini, sai mutumya kasance kamar wani sabon jariri, mutum ya samu gyaran jikin shi. An cire wani abu an kuma mayar da wani, wato an ja jini,an nkumamayar da wani jinin. ‘’Yawancinmata suna mutuwa lokacin haihuwa, a sanadiyar jinin da suke asara, bamu da isasshen jini a Nijeriya, ina ganin ya kamata a sa amaganar bada taimakon jini a Hukumar kula da ishorar lafiya ta kasa (NHIS)’’.
Yayi kira da ‘yan Nijeriya su ci gaba da bada taimakon jini.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: