Wata sanarwa a ranar Lahadi daga fadar shugaban kasa dauke da sa hannun Abiodun Oladunjoye ta bukaci dukkanin gidajen rediyo da kafafen yada labarai na zamani da su kama tashar NTA da Rediyon Nijeriya kai-tsaye domin yada jawabin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai yi.
Tinubu zai yi jawabin ne ga al’ummar kasa wanda za a watsa kai-tsaye a ranar Litinin, 12 ga watan Yuni, 2023, da karfe 7 na safe domin tunawa da ranar dimokradiyya ta bana.
An umurci gidajen Talabijin, gidajen rediyo, da sauran kafafen yada labarai na zamani da su kama tashar Talabijin ta NTA da Rediyon Nijeriya domin yada shirye-shiryen.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp