Wannan takarda gudunmuwa ce ga al’umma masu kishin harshen Hausa, domin a gyara matsalolin da ke damunsa musamman koma bayansa a jami’o’i.
Takardar ta kawo matsalolin, ta bayyana gudunmuwar harshen, sannan ta bayar da shawara ta yadda za a inganta shi.
- Ɗan Nijeriya Ya Lashe Lambar Azurfa A Gasar Ninkaya Ta Duniya
- Ranar Hausa: Yadda Hausawa Ke Tunƙaho Da Harshensu A Faɗin Duniya
Har ila yau, ta tattaro wasu bayanai daga abin da malamai suka riga suka yi.
Amma fahimta daban-daban ake da ita, ni a mahangata zan yi bayani ta fuskoki uku.
Na sa mata suna “Ba Ka Iyawa, Duk Dagewarka, Ba A Yaba Maka (Dankali Sha Kushe)” saboda irin ƙalubalen da harshen yake fuskanta daga gwamnati, malamai, da al’ummar Hausawa da ke jan kafa ga masu nazartar harshen duk da gudunmuwar da suke bayarwa ga al’umma, gwamnati da addini.
Na yi imani babu rayuwa ba tare da harshe ba, domin duk wata al’umma tana da buƙatar harshe domin gudanar da rubuce-rubuce, kimiyya da fasaha.
Amma an yi sakaci da nazarin harshen Hausa, duk da cewa yana cikin manyan harsunan duniya masu ƙarfi da adabi.
Don haka zan fara bayyana matsalolin, sannan in kawo shawarwari.
Matsala ta farko: Sai Bango Ya Tsage…
Idan gwamnati da manyan al’umma ba su ɗauki Hausa da muhimmanci ba, ba zai samu ci gaba ba. An taɓa samun shugaban ƙasa da ya ce nazarin wasu darusa ɓata lokaci ne, amma shi kansa a lokacin yaƙin neman zaɓe da Hausa yake magana.
Gwamnati ta nuna rashin kulawa da harshen Hausa, tana ganin ba shi da amfani. Alal misali:
1. Mayar da Hausa “zaɓi” a sakandire.
2. Tsaurara sharuɗa wajen shiga jami’a domin nazartarsa.
3. Rashin bayar da tallafin karatu kamar yadda ake yi wa wasu harsuna.
Matsala ta biyu: Ka Ƙi Naka, Duniya Ta So Shi
Da yawa daga cikin Hausawa ba sa alfahari da harshensu. Maimakon su zurfafa a kansa, sai ƙasashen waje suka ɗauki Hausa suna koyarwa a jami’o’in duniya. Haka kuma, yawancin Hausawa idan suna amfani da shafukan sada zumunta, rubuce-rubucensu da Hausa suke yi, ko littattafan addini sai an fassara musu da Hausa.
Abin kunya ne a ce ƙasar Nijar ta ayyana Hausa a matsayin harshen ƙasa, amma Nijeriya ba ta yi haka ba, duk kuwa da cewa Hausa na daga cikin manyan harsunan ƙasar.
Haka kuma wasu malamai suna sa wa ɗalibai wahala wajen nazarin Hausa, suna ƙauron da su daga koyonsa.
Matsala ta uku: Idan An Bi Ta Ɓarawo…
Ya kamata malamai da ɗalibai su ci gaba da aikin fassara kalmomi daga fannoni daban-daban na ilimi zuwa Hausa, don a samu damar shiga kowanne fanni kamar yadda ake yi da Turanci, Larabci, Sinanci da sauransu.
Gudunmuwar Harshen Hausa:
1. An fassara kusan duk littattafan addini zuwa Hausa.
2. An fassara littattafan kimiyya, tarihi, lissafi da sauransu.
3. Hausa ta mamaye kafafen sada zumunta kamar Facebook, WhatsApp, X, Instagram da TikTok.
4. Ana amfani da Hausa a kafafen yaɗa labarai a ƙasashe irin su Amurka, Sin da Faransa.
5. Malamai sun rubuta littattafai da muƙaloli da dama domin ci gaban harshen.
Shawarwari:
1. A tafiya da zamani wajen koyar da Hausa.
2. A sauƙaƙa hanyoyin koyo da koyarwa.
3. A mayar da Hausa darasi na dole a firamare da sakandire.
4. A wajabta wa ɗaliban ƙasashen waje koyon Hausa idan suka zo karatu a Nijeriya.
5. A shigar da Hausa cikim fannin kimiyya da fasaha.
6. A sa Hausa cikin darussan GES/GSE a jami’o’i da kwalejojin ilimi.
7. A ayyana Hausa a matsayin harshen hukuma a Arewa ko Nijeriya baki ɗaya.
8. A ƙarfafa gwiwar iyaye, abokai da malamai ga ɗaliban da ke nazartar Hausa.
9. A riƙa bai wa masanan Hausa aikin da ya dace da su, musamman fassara da rubuce-rubuce.
Idan aka aiwatar da waɗannan, za a dawo da martabar harshen Hausa.
Kammalawa
Takardar ta nuna matsalolin da harshen Hausa ke fuskanta, gudunmuwar da yake bayarwa ga al’umma da addini, sannan ta kawo hanyoyin da za a bi don dawo da martabarsa a ƙasar nan.
Mubarak Idris Jikamshi ne ya rubuta albarkacin Ranar Hausa ta Duniya
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp