Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Alhamis, 1 ga watan Mayu, 2025, a matsayin hutu na domin murnar ‘,Ranar Ma’aikata’ ta wannan shekara, wanda ake gudanar da ita kowace shekara domin girmama gudunmawar ma’aikata.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana wannan hutu a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.
- Wang Yi: Neman Sulhu Da Ja Da Baya Riba Ne Ga Masu Son Cin Zali
- Sin Ta Harba Sabon Tauraron Dan Adam Na Ayyukan Sadarwa
Ya yaba da aikin da ma’aikata suke yi da kuma haɗin kai da suke bayarwa wajen ci gaban cikin gida da na waje na ƙasar.
Ya jaddada cewa zaman lafiya da Æ™irÆ™ire-Æ™irÆ™ire suna da muhimmanci wajen cimma ci gaban tattalin arziÆ™i da masana’antu.
Ministan ya kuma buƙaci ma’aikata su rungumi al’adar ƙirƙire-ƙirƙire da inganci a cikin aikinsu, yana mai cewa dagewarsu tana da muhimmanci wajen gina ƙasa.
Ya bayyana cewa ya zama dole a daga matakan kowace sana’a don inganta mulki da kuma tabbatar da cewa ‘yan Æ™asa suna cin gajiyar albarkatun Æ™asar da kyau.
Tunji-Ojo ya sake tabbatar da cewa gwamnati ta yi tsayin daka wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi na ‘yan ƙasa yana mai cewa gwamnatin shugaba Bola Tinubu tana da niyyar aiwatar da alƙawuran da aka ɗauka ta hanyar Shirin Sabuwar Fata.
A ƙarshen, Ministan ya taya ma’aikata murnar wannan rana, yana mai ƙarfafa musu gwiwa da cewa su ci gaba da kasancewa masu gata nagari yayin da ƙasar ke da niyyar samar da ababen more rayuwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp