Connect with us

HANGEN NESA

Ranar Matasa Ta Duniya: Abin Allah Wadai A Nijeriya

Published

on

Ranar 12 ga watan Agusta ita ce ranar da Majalisar dinkin duniya ta ware a matsayin ‘ranar matasa ta duniya’, rana ce da ake tunawa da gudunmawar da matasa suke dashi wajen ginuwar kowace kasa, karfafa dimokradiyya tare da kulla dangantaka tsakanin auratayya, yaduwar jinsi tare da karfafa zaman lafiya.
Su waye MATASA? Majalisar Dinkin Duniya ta fassara kalmar matashi a matsayin me matsakaicin shekaru daga Shekara 15 zuwa 25, shi kuwa wani masanin halayyar dan Adam ‘’ Kehily ‘’ yac e Matashi shi ne wanda ya fara rayuwa daga karkashin iyayensa zuwa tafiya gidan nasa auren’’.
Hukumar dake kula da hakkin matasa ta NYP ta fassara Matasa a matsayin ‘’ samarin dake rayuwa daga shekara 15 zuwa 40’’. Manyan Malamai da marubuta sun fi karkata akan Matasa sune wanda suka fara mallakar kawunansu, wato daga balagarsu zuwa shekara 40, shi ne mutumin dayasan mene ne rayuwa, kuma yake karfafa yau (present) dinsa don cimma gobensa (future life).
Idan har haka ne to ni ‘ Mailafiya ‘ ina cikin Matashi da ya ke cikin miliyoyin matasa a wannan kasa; kamar yadda Shugaban Majalisar Dinkin Duniya ya jinjinawa matasa a jawabinsa, ‘’ ya karfafi gwuiwarmu domin cimma Nasarar rayuwarmu, juriya wajen neman Karatu da kuma harkokin Kasuwanci, karfafa dangantaka tsakanin Kabilu, bautawa kasarmu da duk karfinmu domin raya dimokradiyyar kasarmu’’ hakika Kalaman irin mutanen nan sun fi kama da sauran matasan dake rayuwa a wata duniya, ba irin duniyata ta Nijeriya ba.
Matasa dake rayuwa a kasar Nijeriya sun fi kowa samun kansu cikin tashin hankali da kaskantacciyar rayuwa, sun fi kowa samun kansu cikin halin kunci da rashin Sukuni sakamakon zalunci da suka tsinci kansu daga Shugabanninsu, sun tsinci kansu cikin rashin samun wadataccen Ilimi, sun rasa tagomashin dogaro kansa, yawancinsu suna rayuwane daga wani bigire na zafin zuciya zuwa bigiren rayuwa cikin dacin zuciya, a iya kiyasina na mutane Miliyan 160 a kasata na Nijeriya, idan ka kiyasta zakaga za’a iya samun adadin matasa miliyan 80 amma maza da matanmu, idan ka kiyasta cire adadin maza daga na mata zaka iya samun adadin maza miliyan 45, a kawai wannan adadin akalla matasa miliyan 41 suna rayuwane a kaskance wacce a irin arzikin Kasar Nijeriya sun wuce irin wannan rayuwa, Misali acikin adadin Miliyan 41, kaso 3 daga cikinmune suke makaranta daga aljihun gwamnati zuwa makarantun Jami’o’i, sune kawai iya adadin wanda iyayensu suka iya daukan nauyinsu, kaso 1 daga cikinmu kuma sune wadanda iyayensu masu hannu da shuni ko kuma jami’an gwamnati ne, suka tura su kasashen ketare domin samun nagartaccen ilimi,sannan kaso 1 kuma daga cikinmu sune suke iya rungumar harkar kasuwanci kuma suke daddafawa,kuma acikinsune wasu suke iya samun aikin gwamnati watakila ma sai da suka bada cin hanci suka samu, a jimlace kaso 5 kenan cikin 10, yayinda kuma ragowar kaso 5 din suke gararambar rayuwa, domin kuwa kaso 1 ne suke wahalalliyar rayuwa akarkashin iyayen gidansu, ko kuma aikin kamfanunnuka a karkashin masu kudin kasar nan, kaso 4 hudu kuwa ba su da aikin yi ballantana wurin zuwa, basa karatu kuma basa sana’a, karatun ya fi karfinsu ballantana su yi fatan samun aikin gwamnati, sannan suma sauran kaso Ukun dasuke iya karatun, Kaso daya ne daga cikinsu suke iya samun aiki idan sun gama, watakila ko don alfarmar ‘yan siyasa ko kuma bisa tsananin rabo daga Allah Mai Girma, ka ga kenan kaso bakwai daga Kashi 10 ba su da tudun dafawa a wannan kasa, kuma wannan Kiyasi nawa (ni Mailafiya) shi ne kiyasi dake tafiya tsahon Shekaru 10…..kuma duk suna rayuwane acikin Kasar datafi kowa Karfin Tattalin arziki a Nahiyar Afrika, itace wacce take Cikin Kasashe Masu arzikin Man fetur na Duniya, itace kuma Kasar dake datake kiranta Kanta Giwar Afrika, wadda ta tara Manyan Mashahuran Masu Arzikin a Arzikin Duniya irinsu O’ o da wancananka.
A tsahon Shekara 1 daga wancan Agustan bara zuwa wannan Agustan na ziyarci garuruwa dayawa musamman Arewaci da wasu daga cikin kudu, Mafi girman garin Kasuwanci a Nijeriya shi ne Lagos da Kano, naje Lagos kuma ni Mazaunin Kano ne, hakika Matasanmu suna cikin garari da gararanbar rayuwa, aikin yi yagarari dubunnan matasa, ilimi kuwa yazama sae wane da wane, Uwa uba ga Kisan Kiyashi da kullum ake yi wa Matasa daga ‘yan Boko Haram.
Matasa Shingen Aikata Laifuffuka
Ko kuma ba ina aibanta Matasan Kasata bane, a’ah kawai Inason hasko yanda muke kaskantacciyar rayuwane saboda Samun Butulun Shugabanni, Mayaudara kuma Azzalumai, wadanda basu san kowaba sai Kansu da ‘Yayansu, wadanda suka ci Amanarmu da Kundin tsarin Mulki, dole nayi Allahwadai da aikinsu, nakuma Aibatasu tunda inada ‘Yanci akansu. Idan aka kama ‘barawo to zakaga Matashi ne, rashin Sana’a ne yajawo Masa, idan aka Kama Dan Fashi shima matashi ne,rashin samun aiki shi ne ya Janyo masa, watakila ma yanada digirin-digirgir…..karshe gun wanda yaje yin fashin jami’in gwamnatine dake satar kudin Kasa, watakila ko Kwalin karatu me kyau bashida shi…..kai Allah Wadaran Naka ya lalace.
Ina dai taya sauran matasan Duniya murnar zagayowar RANAR MU. Amma mu a nan MU NA BAKIN CIKI DA ZAGAYOWARTA
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: