Daga Abdullahi Muhammad Sheka
A yayin da a ke bikin ranar yaki cutar kanjamau ta duniya a ranar Talatar data gabata, Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama maza da mata kimanin 40, wadanda ke dauke da cutar Kanjamau kuma suke yada ta ga sauran jama’a a jihar.
Kwamandan Hisbah na jihar Kano, Malam Muhammad Harun Ibn Sina, ne ya bayyana haka, inda ya ce sun kama mata guda 32, sai kuma maza guda 10. Hukumar ta kama mutanen ne a kasuwar saida kayan gwari ta garin Badume da ke karamar Hukumar Bichi a jihar ta Kano.
Ya ce, mutum bakwai daga cikin matan sun san su na dauke da cutar, yayin da kuma ragowar matan sun fahimci hakan ne bayan sakamakon gwajin da a ka yi mu su ya fito. Ya ce, bayan da a ka bayyana mu su hakan ne, sai kuma su ka barke da kuka sakamakon rashin sanin cewa, su na dauke da cutar ta Kanjamau.
Ya cigaba da cewa, wasu daga cikin wadanda a ka kama din ba ’yan asalin Jihar Kano ba ne, sun zo ne daga makwabtan jihohi.
Majalisar Dinkin Duniya dai ta ware ranar daya ga watan Disambar kowace shekara a matsayin ranar cutar kanjamau ta duniya, don nuna goyan baya ga mutanen dake dauke da cutar da kuma tuna wadanda suka rigamu gidan gaskiya a sanadiyyar cutar ta kanjamau.
A cewar Hukumar lafiya ta duniya mutan miliyan 38 ne ke dauke da cutar ta kanjamau a fadin duniya. Haka kuma fiye da kaso sittin na wadannan mutane sun fito ne daga najiyar afrika.