Shugaba Bola Tinubu zai yi wa ‘yan ƙasa jawabi a ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba, 2025, don murnar cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai.
Sanarwar ta fito ne daga Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, wanda kuma ya ƙaddamar da kwamitin shirya bukukuwan ranar.
- “Hadin Kan Kasashen BRICS” Ya Karfafa Shawo Kan Kalubale
- Jami’ar MAAUN Da Kwalejin Seneca ta Canada Sun Yi Haɗin Gwiwa Domin Samar Da Damarmaki Ga Ɗalibai A Duniya
SGF ya ce Ranar ‘Yancin Kai lokaci ne na tunani kan ƙalubale da nasarorin Nijeriya da kuma shirin makomarta.
Bukukuwan za su fara da Taron Manema Labarai a ranar 25 ga watan Satumba, sai tarukan addini, ayyukan mata da matasa, nune-nunen fasaha, da karatun jama’a.
Bukukuwan za su ƙare da jawabin Shugaban Ƙasa da liyafar Ranar ‘Yancin Kai a ranar 1 ga watan Oktoba.
Za a kuma ƙaddamar da sabon shiri, Nigeria@65 Compendium, wanda zai zayyano ci gaban ƙasa a fannoni kamar shugabanci, tattalin arziƙi, da ci gaban ƙasa a tsawon shekarun.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp