Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya kare salon mulkinsa na tsawon shekaru takwas da ya yi a jihar, inda ya jaddada cewa ya tabbatar da adalci da daidaito tsakanin kowane ɓangare, tare da ƙin amincewa da abin da ya kira “haƙƙoƙin mu ne” daga mutanen Kudancin Kaduna.
Da yake jawabi a shirin ‘Sunday Politics‘ na tashar talabijin ta Channels, El-Rufai ya ƙaryata zargin nuna son addini, yana mai cewa manufofinsa sun shafi kowa, ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ba.
- Gwamnatin Tarayya Na Shiri Da Ƴan Bindiga, Tana Ba Su Biliyoyi — El-Rufai
- Sadiq Umar Da Bello El-Rufai Sun Sayi Ƙungiyar Rancher Bees FC Ta Kaduna
Ya bayyana cewa wasu mutane daga Kudancin Kaduna sun saba samun fifiko a ƙarƙashin gwamnatocin da suka gabata, wanda shi ya dakatar da shi da gangan, kana ya zargi wasu shugabannin Kirista daga yankin suna cin moriyar wasu tallafin kuɗi da gwamnatinsa ta daina bayarwa.
Game da batun wakilci a gwamnati, El-Rufai ya musanta iƙirarin wariya, yana mai cewa naɗe-naden muƙaman gwamnati an riƙa yin su bisa daidaito tsakanin kowace mazabar sanata, ba wai bisa addini ko ƙabilanci ba.
Kan batun goyon bayansa ga tikitin musulmi-musulmi na jam’iyyar APC a zaɓen 2023, El-Rufai ya ce tsantsar dabarar siyasa ce kawai, kuma duk wani ɗan siyasa yana tafiya da lissafin yadda zai kai ga samun nasarar ne.














