Daga Sulaiman Bala Idris, Abuja
Ƙungiyar ‘yan ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta bayyana cewa za ta jagoranci zanga-zanga zuwa majalisar ƙasa da kuma Fadar Shugaban Ƙasa, domin su gabatar da koken ma’aikata, dangane da rashin biyan albashinsu da wasu gwamnonin jihohi ke ci gaba da riƙe wa.
Ƙungiyar ‘yan ƙwadagon ta yi kira ga ‘yan Nijeriya da su sa hannu wurin bayar da tallafi ga ma’aikatan da suke bin gwamnonin wasu jihohi bashi.
A yayin da yake zantawa da manema labarai jiya a Babban Birnin Tarayya, Abuja, Shugaban Ƙungiyar ‘yan Ƙwadago, Ayuba Wabba ya bayyana cewa ma’aikata sun faɗa cikin wani irin mawuyacin hali sakamakon rashin biyan albashi.
Ya ce, har an kai wani yanayi da ma’aikata suka gwammace su riƙa kashe kawunansu saboda ba za su iya ɗaukar ɗawainiyar Iyalansu ba. “Muna gargaɗin waɗannan gwamnonin da su kwana da sanin cewa su daina yi mana gani-gani, musamman ma da muka lura da cewa ba a shirye suke a sasanta da su ba.”
Daga ƙarshe Shugaban Ƙungiyar ‘yan ƙwadagon ya yi kira ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da ya bincike badaƙalar dawo da tsohon jangoran hukumar Fansho, Abdulrasheed Maina. Ya ce; “A binciko waɗanda ke da hannu, a hukunta su daidai da laifin da suka aikata.”