Wata babban kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta daure Sufeton Janar na ‘yansandan Nijeriya, IGP Usman Alkali Baba, watanni uku a gidan yari bisa rashin mutunta umarnin kotu.
A hukuncin da alkalin kotun Mai Shari’a M. O. Olajuwon ya yanke, ya ce IGP din zai kasance a gidan yari kuma a tsare na tsawon watanni uku, ko kuma har sai ya bi umarnin da kotun ta bayar tun ranar 21 ga watan Oktoban 2011.
Wannan matakin na zuwa ne bayan da wani jami’in dan sanda, Mr. Patrick Okoli ya shigar da kara bisa zargin cewa hukumar ‘yansandan Nijeriya ta masa ritayar dole kuma ba bisa ka’ida ba.
Mai Shari’a Olajuwon ya lura kan cewa, duk da hukumar kula da harkokin ‘yansandan (PSC) ta bada shawarar a maida Okoli cikin jami’an ‘yansanda biyo bayan umarnin hakan da kotu ta bayar, amma Sufeton Janar din ya ki bin wannan umarnin.
Sannan kotun ta kuma umarci a bai wa mai karar naira miliyan 10 a matsayin barnar da aka masa bisa, take masa hakki da bin lamura ba bisa ka’ida ba.