Atatullahi Tage daya daga cikin jarumai a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood a wata hira da yayi da jaridar DCL Hausa a cikin shirinsu na sirrin daukaka ya tabo batutuwa da dama da suka shafi masana’antar ciki har da abin da ya kira shamaki ga ci gaban wannan babbar masana’anta da dubban al’umma ke neman abinci a cikinta.
Ni dai an haife ni a jihar Jigawa wanda cikin ikon Allah zama ya dawo dani nan Kano, sakamakon mahaifina da yake zaune a nan tsawon lokaci, abubuwa da dama sun sa ban yi zurfi a karatun zamani ba domin kuwa ko makarantar Sakandire ban kammala ba ko da na bar zuwa makaranta in ji Ayatullahi.
- Me Ya Sa Fina-finai Masu dogon Zango A Masana’antar kannywood ke Zama Cin kwan Makauniya?
- Kallo Daya Mutum Za Yi Min Ya Gane Masana’antar Kannywood Ta Canza Rayuwata -Farida Abdullahi
A lokacin da na zo Kano na yi sana’oi da dama kafin in zama abin da na zama a yanzu kama daga tallar kaset a baro, inda nike zuba kaset-kaset a baro ina zagayawa ina sayarwa, daga wannan sana’a ce na dawo harkar fim gadan-gadan, a wancan lokacin ban gamu da wani cikas yayin shigata harkar fim ba kamar yadda nike ji wasu na fadin matsalolin da suka fuskanata yayin shigiwa.
Dalili kuwa shi ne ko da na fara wannan harka ta fim bani da wani wanda ke tsawatar mani sakamakon iyayena da suka rasu, a wancan lokacin ma ba kowa ne ya damu da abin da na samu ko ya sameni ba, wasu mutane ma kallon wani mutum marar amfani suke yi mani, da haka dai na ci gaba da dagewa har Allah ya kawo ni inda nike yanzu ya kara da cewa.
Da yake amsa tambaya akan minene sirrin samun daukakarshi Tage ya ce ba komai ba ne sirrin samun daukaka illa Hakuri, Biyayya da kuma aiki tukuru, domin kuwa idan ka saka wadanann a zuciyarka to komai zai zo maka a cikin sauki ba tare da ka wahala ba, yanzu sau da dama mutane sun fi son su samu abu cikin sauki kuma cikin lokaci ba tare da sun wahala ba.
Sai kaga mutum daga ya samu wata yar dama to do yake ace ya samu wata hanyar wulakanta wannan wanda yayi masa rana kokuma ya wuce shi a matsayi ko wani abin Duniya ba tareda la’akari da cewar wannna wanda ya koya maka to ya fika sanin komai a wannan harkar musamman ma a nan masana’antar Kannywood.
Don haka kamata ya yi ce mutane sun fahimci cewar babu ta yadda za a yi ka ci gaba matukar ka na da wata niyyar cin amanar wanda ya taimake ka ka kai wani matsayi na rayuwa, ni yanzu a matsayina na Ayatullahi Tage na yi biyayya ga maigidana Alhaji Tage wanda ya nuna mani hanya, ya rike ni kamar dan da ya haifa, kuma yake fatan duk wani alheri na Duniya ya same ni.
Ga shi yanzu ina ganin amfanin biyayyar domin kuwa duk wani abin da ake fatan samu na alheri a wannan masana’antar Allah ya nufe ni da samu kama daga mutunci, daukaka da kuma abin Duniya, don haka nike shawartar ‘yan uwa abokan sana’ara da ma sauran mutane da su kasance masu biyayya a duk inda suka samu kansu a rayuwa kuma kada su zamo masu girman kai ko nuna kyashi ga abin da wani ya samu domin kuwa Allah mai iko ne akan kowa da komai zai iya baiwa wanda bai da shi, ya kuma amshe ga wanda ke da shi idan yaga dama.
Dangane da matsaloli ko kalubale da masana’antar Kannywood ke fuskanta Tage ya ce, ba komai ya janyo hakan ba illa rashin hadin kai a tsakanin masana’antar, duk al’ummar da aka ce babu hadin kai a tsakaninsu to lallai za ka samu wannan al’umma babu wani cigaba da suka samu, to amma matukar muka hada kanmu ya zamana mun zamo tsintsiya madaurinki daya babu wata baraka da za ta iya shigowa a cikinmu ya tabbatar.
Muddin aka ce akwai hassada ko kyashi a tsakaninmu to zai yi wuya mu dinga bai wa junanmu shawarwarin da za su ciyar da masana’antar gaba, sakamakon haka kuwa ba karamar illa zai janyo mana ba, don haka nike kira ga mahukunta da sauran al’umma da ke cikin Kannywood da mu daure mu hada kanmu domin mu kai wannan masana’antar inda ya kamata ta kasance.
Daga karshe ya bukaci mutane da ke furta kalaman tsinuwa ga jaruman fim da suji tsoron Allah su bari, idan kuma ba haka ba to su sani cewa su kansu basu san wadanda za su haifa ba, mai yiwuwa su haifi yaron da zai ji ya na sha’awar harkar fim kuma ya shigo harkar a dama dashi, to idan haka ta faru wannan tsinuwar da sukayi wa jaruman fim za ta shafi yayansu da suma suka shiga cikin harkar fim din.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp