Asusun bayar da lamuni na duniya (IMF), ya bayyana damuwa kan yadda rikicin kasuwanci tsakanin Amurka da China ke barazana ga ci gaban tattalin arziƙin duniya.
A wani rahoto da aka fitar ranar Talata, IMF ta ce waɗannan ƙasashe biyu da ke riƙe da madafun iko a harkokin tattalin arziƙin duniya suna haddasa matsaloli da ka iya jefa duniya cikin koma baya.
- Sin Ta Bukaci Amurka Ta Daina Siyasantar Da Batun Asalin Cutar COVID-19
- An Kimtsa Tsaf Don Kaddamar Da Aikin Binciken Kumbon Shenzhou-20 Na Kasar Sin
Rahoton ya bayyana cewa harajin da Amurka ke ƙaƙaba wa China da wasu ƙasashe na hana walwalar cinikayya da ke da muhimmanci ga ci gaban duniya.
Kamar yadda rahoton ya nuna, IMF ta rage hasashen yadda tattalin arziƙin duniya zai tafi a shekarar 2025, inda ta ce maimakon a samu kashi 3 na ci gaba, za a samu kashi 2.8 ko ƙasa da haka.
Har ila yau, ana ganin cewa a shekarar 2026 tattalin arziƙin duniya zai shiga wani mawuyacin hali fiye da yadda aka zata.
Shugaban sashen tsare-tsare na IMF, Pierre-Olivier Gourinchas, ya shaida wa manema labarai cewa duniya na shiga wani sabon lokaci na ruɗani a fannin tattalin arziƙi, wanda zai iya rushe tsarin da aka shafe kusan shekaru 80 ana ginawa.
Ya ƙara da cewa harajin da ƙasashe ke ƙaƙaba wa juna da kuma rashin tabbas a manufofin kasuwanci suna daga cikin manyan dalilan da ke kawo wannan koma baya.
Rahoton na IMF na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan gwamnatin Amurka ta ƙara wasu sabbin haraji kan kayayyakin da ke shiga da su ƙasar daga waje, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin masana da ƙasashe masu ruwa da tsaki.
IMF ta shawarci ƙasashen duniya da su zauna a teburin sulhu domin kawo ƙarshen rashin jituwa da ke hana ci gaban tattalin arziƙi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp