Daga Muazu Hardawa, Bauchi.
An bayyana rashin wadatar masana’antu a kowace kusurwa ta Nijeriya a matsayin babbar matsalar da ke barazana ga rayuwawar matasa, lamarin da ke sa ƙ aruwar masu zaman kashe wando. Sarkin Wandi a ƙ aramar hukumar Dass Alhaji Mohammed Bello Manda Aliyu,
ne ya bayyana haka cikin hirarsa da wakilinmu a Bauchi, inda ya ƙ ara da cewa, matuƙ ar ana son shawo kan matsalar tsaro da rashin aiki, dole sai gwamnatoci sun haɗa kai da masu hannu da shuni an sauƙ aƙ a hanyoyin ƙ irƙ iro da manya da ƙ ananan masana’antu, waɗanda kuma suka
durƙ ushe, ta hanyar samar da kuɗin farfaɗo da su.
zamanto abokin shawarar su, daga nan sai jin haushin masu mulki da ‘yan siyasa da duk wani mai abin hannu. Matsala kaɗan idan ta taso sai matasan su karaya duka ta hanyar yin abin da zuciyarsu ta raya musu.
Don haka ya shawarci shugabanni su sake tsarin hanyar samar da ayyukan yi ga matasa a fitar da kuɗi a raba wa ‘yan kasuwa da manoma tsakani da Allah ta yadda za su gina kamfanoni manya da ƙ anana da gonakin noma da kiwon dabbobi da kifi da kaji don a samu hanyoyin samar da ƙ arin ayyukan yi ta yadda za a rage yawan matasa masu zaman kashe wando.
Mohammed Bello, ya ƙara da cewa, duk yawan abin da za ka ba matashi, idan ba ka samar da wajen da zai zauna na tsawon awoyi a wuni ba, to shaiɗan ne zai kasance abokin shawararsa a duk lokacin da ya kasance shi kaɗai ba tare da sanin tudun dafawa ba.
Haka kuma ya shawarci iyaye su tashi tsaye wajen tarbiyyantar da yaransu, musamman ganin an
shiga cikin wani yanayi da a kullum haihuwa ake yi, abin da ake samu don buƙ atun yau da kullum kuma baya wadatarwa, hakan ke sa wasu iyayen ba sa sanin me ‘ya’yan su ke yi don
gudanar da rayuwa, kowa ya zamo da inda ya sa gabansa. Don haka ya shawarci matasan da iyaye kowa ya koma kan noma da karatu da kuma sana’ar da aka gada tun farko don a magance matsalar da ake ciki ta lalacewar tarbiyya da aikata miyagun laifuka daga matasasan.
Harwa yau, ya shawarci ‘yan siyasa su daina amfani da matasa wajen banga da neman tayar da hankulan mutane saboda wasu muradu na kai ko na neman matsayi don a samu ciyar da ƙ asa gaba da gina al’umma.