Idris Aliyu Daudawa" />

‘Rashin Motsa Jiki Yana Kara Kusantar Da Kamuwa Da Cutar Zuciya’

Wani sabon bincike wanda aka kuma wallafa shi a mujalla mai suna European Heart Journal wato wadda ta shafi al’amarin zuciya, ta bayyana cewar rashin motsa jiki, yana iya sanadiyarb yiyuwar kamuwa da cutar zuciya daga karshe, koda kuma ace yanzu ba wasu alamu da suke nuna hakan ayanzu.
Masu binciken sun duba lafiyar fiye da mutane 4,500 wadanda suka kasance cikin binciken wanda ake kira da suna HUNT3 kamar dai yadda mujallar al’amuran lafiya na yau ta bayyana. .
Ba wani daga cikin wadanda suka halarci shi binciken yake da tarihin ita cutar wadda kuma tajke da nasaba da zuciya, cutar Huhu, kansa ko kuma ciwon daji, kuma hawan jini, lokacin da aka yin binciken.
Fiye da kashi 50 na wadanda suka halarci taron mata ne wadanda kuma fiye da kashi 80 nasu, suna da rashin yiyuwar kamuwa da cutar har nan da zuwa shekaru goma masu zuwa.
Wani daga cikin marubutan na karshe dangane da shi binciken Dokta Bjarne Nes ya bayyana cewar su masu binciken sun yi amfani ne da, kayan binciken daya kamata, ko kuma isasshen iska wanda ya dace a shaka, cerwar a gwada su wadanda suka wajen taron n bincike, wato yadda al’amarin daya shafi jikin su yake.
Nes ya ci gaba da bayani cewar yawan ko mizanin iskar data kamata a sha, da kuma, wadda ta mata shi jiki ya samu lokacin da aka motsa jiki.
Daga karshen shi binciken na wadanda suka halarci shi binciken suna da matsalolon da suka shafi zuciya, ko kuma suna dauke da cutar angina pectoris, wadannan matsaloli ne wadannda za ‘a iya fuskanta a dalilin rufewar ko kuma tsukewar wadansu jijiyoyi masu aikin kai jini duk wurin daya kamata.
Nazarin da nasu binciken suka yi ya nuna alakar da ake da ita,tsakanin jada bayan yiyuar kamuwa da cutar matsalar data shafi zuciya da kuma, samun ci gaba na ingancin jiki kamar yadda ya kamata.
Nes ya ci gaba da bayanin cewar “Koda ma tsakanin mutane wadanda ake tsammanin suna da lafiya, kashi 25 na irin wadannan mutanen, irin su su kan ko kuma suna iya kasancewa rabi, ko kuma a kalla kashi 25 nasu.
“ An gano da ata babbar alaka tsakanin wadanda ake ganin basu iya kamuwa da cutar da kuma hawan jini ko kuma bugun zuciya, ko kuma angina pectoris, a shekaru 9 da suka wuce, wannan kuma ya biyo bayan gwajin nasu da aka yi.
“ Mun kuma san marasa lafiya wadanda suke da basu shakar iska yadda ya dace, suna da yiyuwar mutuwar farar daya ko kuma cutar zuciya.”

Exit mobile version