Abba Ibrahim Wada" />

Rashin Ronaldo Yasa Magoya Bayan Real Madrid Sunki Zuwa Kallon Wasa

A karon farko cikin shekara 10 magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid sunki zuwa kallon wasan kungiyar sai dai kungiyar tasamu abinda takeso bayan tasamu nasara daci 2-0 a wasanta na farko na laliga babu Ronaldo.

Carbajal da Gareth Bale ne dai suka zura kwallayen guda biyu a ragar Getafe wanda hakan yasa sabon kociyan kungiyar Julian Lepatugui, yasamu nasara a wasansa na farko a kungiyar ta Real Madrid a wasannin laliga.

Magoya baya dubu arba’in da takwas da dari hudu da sittin da shida (48,466) ne kawai sukaje kallon wasan na Real Madrid bayan da akayi zaton sama da magoya baya dubu 70 zasu shiga kallon wasan na farko.

Wannan ne karo na farko da magoya baya basu shiga filin wasan kungiyar ba tun kakar wasa ta 2008 zuwa 2009 shekarar da kungiyar tayi rashin nasara a wasanni shida a jere ciki har da rashin nasara da kwallaye 6 a hannun Barcelona.

Magoya bayan kungiyar sunki shiga filin wasanne saboda babu Cristiano Ronaldo wanda kungiyar ta siyar zuwa Jubentus a watan daya gabata sannan kuma babu sabon dan wasan da zasuje domin su gani.

Mai tsaron ragar da kungiyar ta siya ma daga Chelsea, Thibaut Courtois har yanzu bai fara buga wasa ba hakan yasa magoya bayan kungiyar dole su sake jira sai wasan gaba ko mai koyarwar zaiyi amfani dashi.

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dai har yanzu tana neman abbban dan wasan da zau maye mata gurbin Ronaldo inda tuni ta nemi dan wasa Edin Hazard na Chelsea kuma yanzu yace bazai bar kungiyarsa ba.

Exit mobile version