Daya daga cikin tsoffin mawaka da suka dade ana damawa dasu a masana’antar Kannywood kuma wanda ya shahara a wannan fanni na waka a shekarun 2010-2015 Aminu Mai Dawayya ya magantu a kan wadanda ke karyata shi dangane da maganar da ya yi na cewar a tsawon shekarun da ya shafe a harkar waka ya samu kyautar motoci har guda 75 daga wajen masoyansa.
Mai Dawayya wanda ya tabbatar da cewar a duk cikin mawakan da suke a Arewacin Nijeriya na da da na yanzu babu wani wanda ya kai shi samun kyautar mota in banda marigayi Dakta Mamman Shata, inda ya ce bayan wadannan adadin da ya samu akalla ya sayi motoci kimanin 70 da kudin alhihunsa domin kuwa a wancan lokacin yadda ya ke daukar hular kan sa haka ya ke daukar motar hawa duk da cewar yanzu bashi da mota sakamakon yanayin rayuwa.
- Muna Samun Nasarori A Yaki Da Gurbatattun Masana’antar Kannywood – Tijjani Asase
- CCCEU: Harajin EU Kan Motocin Lantarki Zai Kawo Cikas Ga Burin Daidaita Sauyin Yanayi
A hirar da ya yi da jaruma a masana’antar Kannywood Hadiza Gabon a cikin shirinta mai suna Gabon’s Room Talk Show Aminu ya ce bai so sake magana dangane da wannan ikirari na mallakar motoci da ya yi a baya ba, domin kuwa akwai wasu wadanda basu san wanene shi a lokacin baya ba suna karyata wannan magana da ya yi inda wasu ke cewa ko a gidan gwamnati ba kowanne ake samun adadin wadannan motoci da Mai Dawayya ya yi ikirarin mallaka ba.
Ba abin mamaki ba ne idan nace na samu kyautar mota 75 daga hannun masoya na, kuma na sayi kimanin 70 da kudi na ba domin kuwa a masana’antar Kannywood, ni na fara hawa motar kaina hakazalika ni ne mutum na farko da ya fara zuwa kasar Saudiyya domin sauke farali a wannan masana’antar tamu ta Kannywood inji Mai Dawayya.
Amma saboda yanzu yanayin rayuwa ya canza bani da mota ko daya yasa idan na yi waccan maganar sai wasu su dinga nuna rashin amincewarsu, wannan kuma rashin sani ne kawai domin kuwa da ace sun san wanene Mai Dawayya a shekarun da suka gabata da basu yi wannan magana ba ya kara da cewa.
Dangane da bacewar muryarsa a masana’antar Kannywood kwana biyu, Aminu ya ce ba bacewa muryarsa ta yi ba kawai dai sun ja da baya ne domin wasu su bai wa matasa masu tasowa dama suma su nuna tasu bajintar da Allah ya basu, amma yanzu ya dawo bakin aiki inda zai ci gaba da nishandantar da masoyansa da wakoki kamar yadda ya saba a baya.
Mai Dawayya ya bukaci matasan mawaka masu tasowa a masana’antar Kannywood da su tabbatar sun yi amfani da wannan lokaci da suke kan ganiyarsu kuma Duniya take yi dasu wajen gina gobensu, ba wai su dinga hawan motoci da sauran sharholiyar rayuwa ba har lokaci ya zo ya kure masu basu ankara ba.