• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rashin Tabbas Ya Dabaibaye Dorewar Aikin Noma Da Gwamnatin Buhari Ta Kirkiro

byAbubakar Abba
2 years ago
Buhari

Shekaru da dama da suka wuce,  fannin aikin noma  a kasar ya fuskanci kalubale da dama da suka hada da rashin zuba kudi a fannin.

Sai dai,  labarin ya canza tun a shekarar 2016 bayan da gwamnatin shugaban kasa  Muhammadu Buhari ta zuba biliyoyin Naira a fanin aikin noma.

  • INEC Ta Raba Muhimman Kayyayakin Zabe Don Kammala Zaben Gwamnan Kebbi
  • Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Kasar Brazil

Gwamnatinsa ta zo da sabbin tsare-tsare da shirye-shirye domin bunkasa aikin naoma da samar da wadacaccen abinci a kasar, musamman domin a Nijeriya ta rage yin dogaro akan shigo da amfanin gona zuwa cikin kasar nan daga ketare, inda hakan ya sa aka samu rage kashe biliyoyin dalar Amurka don shigo da amfanin.

Wasu daga cikin shirye-shiyen da gwamnatin ta kirkiro da su sun hadada, shirin samar da takin zamani na fadar shugaban kasa (PFI), shirin aikin noma na Anchor Borrowers da sauransu.

Sai dai, abin takaici, wasu daga cikin wadannan shirye-shiyen masu kayu, cin hanci da rashawa ya yi masu kakatutu, ko kuma wasu mutanen da ba manoma sun mamaye shirye-shiyen.

LABARAI MASU NASABA

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina

Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo

Misali shirin aikin noma na Anchor Borrowers gwamnatin Buhari ce ta kirkiro da shi a shekarar 2016, wanda a tun da farko gwmanatin ta kebe Naira biliyan  40, don a tallafawa manoman ta hanyar ba su rancen da bai da kudin ruwa.

Tun a wancan lokacin, sama da Naira tirilyan 1.5 aka rabarwa da manoman a a tsakiyar shekarar 2022 a karkashin shirin.

A cewar rahoton da aka fitar a watan da ya wuce, Asusun bayar da lamuni na dunya IMF, ya dora jimlar kan Naira tiriliyan  1.9 tare da kashi 25 a cikin dari kacal da aka karbo, inda kuma ba a iya karbo  Naira tiriliyan 1.4 ba.

Bugu da kari, CBN ta hanyar mukaddashin Darktan sashen samar da bayanai Dakta AbdulMumin Isa ya karyata wannan ikirarin, inda ya jaddada cewa, Bnkin ya karbo kimain kashi 52 a cikn dari na kudin.

Hakazalika, bayan kaddamar da shirin na Anchor Borrowers a 2016, mutane da ba su da wata nasaba da aikin noma, sun ta kafa kungiyoyi kayan masarufi, don kawai su samu rancen kudin na noma.

Misali, a ranar 16 ga watan Maris na 2023, ofishin hukumar EFFC na shiyyar jihar Legas, ta gurfanar da wani mai suna Uche Chigozie Edwin kan damfarar kungiyar masu noman Masara da sarrafa Naira biliyan 1.4.

Har ila yau, akwai kuma zargin badakalar  baya da rance Naira biliyan 5.6 na shirin noman Alkama da ke a karkashin kulawa hukumar (NIRSAL), inda hakan ya janyo aka kori wasu ma’aikatan hukumar daga aikinsu.

Bugu da kari, akwai kuma zargin harkalla a shirin samar da takin zamani na fadar shugaban kasa.

Shugaba Buhari ya kadamar da shirin na (PFI)  a watan Disambar 2016 bisa yakinin kara karfafa sarrafa takin zamani a cikin kasar nan.

Sai dai, abin takaici cin hanci da rashawa ya bulla a cikin shirin, inda hakan ya haifar da rubuce-rubucen korafi kan zargin wasu jam’ian da ke a cikin shirin kan karkatar da kudaden da aka zuba don samar da takin zamani, da suka kai yawan Naira biliyan 300

Hakan ya tilasta gwamnatin tarayya sake yiwa shirin garambawul.

Kusan shekaru biyu ke nan zuwa yanzu, shirin ya zama tamkar na jeka na yi ka, inda takin zaman ya zamowa maomna kasar nan, musamman kananan manoma tamkar Gwal, ganin cewa farashin Buhu daya ya haura Naira 25,000.

Mafitar akan wannan matslar kamar yadda shugaban manoma na gasakiya na kasa Architect Kabiru Ibrahim, dole ne gwamnati tarayya mai zuwa ta yi dukkan mai yuwa don ganin shirye-shiryen sun ci gaba da daorewa

Ibrahim ya kuma shawarci zababben shugaban  kaar mai jiran Gado Boal Tinubu da ya nada minitan aikin gona da raya karkara bisa cancanta wanda kuma ya san yadda daukacin hukomomin aikin noma za su iya gudanar da yyukan su yadda ya kamata.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina
Noma Da Kiwo

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina

October 3, 2025
Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo
Noma Da Kiwo

Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo

October 3, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi

September 27, 2025
Next Post
Ridi, Citta, Zoborodo Na Kan Gaba A Jerin Amfanin Gonan Da Ake Fitar Wa A Tashar Apapa

Ridi, Citta, Zoborodo Na Kan Gaba A Jerin Amfanin Gonan Da Ake Fitar Wa A Tashar Apapa

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025
Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version