Abubakar Abba" />

Rashin Tsari Ya Sa NNPC Tafka Asarar Naira Biliyan 546

Sakamakon gazawar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari akan samar da tsari akan fannin mai da gas, ya janyowa kamfanin NNPC asarar samun kudin shiga har sama da naira biliyan 546.

Lamarin bawai kawai ya shafi gabatar da asarar samarwa da gwamnatin kudin shiga bane ya kuma janyo babbar kalubale ga kasafin kudi na shekarar 2018 da ake sanya rai da kuma wanzar da kasafin. A shekarar 2015, kamafanin ya yi asarar naira biliyan 267.14.

A shekarar data biyo baya kuwa, an samu nukusani na naira biliyan 197 haka kuma a shekarar 2017,bayanai daga na harkar kudi ya nuna cewar, anyi asarar naira biliyan 82 na aiki.

Masu fashin baki a masana’antar, sun bayyana cewar, baya ga rashin samar da tsarin shi kanshi kamfanin na NNPC, shima za’a iya dora masa

laifi.

Sun kuma nuna damuwar su akan rikicin shugabanci a tsakanin karamin ministan mai da albarkantu Ibe Kachikwu da shugaban rukunonin kamfanin NNPC Dakta Maikanti Baru.

Masa fashin bakin sun kuma yi nuni da cewa gazawar majalisar kasa da fadar shugaban kasa wajen shawo kan zargin akan kin bin ka’ida wajen rattaba hannu na kimanin naira biliyan 25 na kwangilar, inda hakan ya nuna cewar, ba’a bin ka’ida a masana’antar.

Koda yake, sun bayyana cewar, shugabancin na yanzu, ya taba dora laifin akan kamfanin NNPC akan shiga harkar kasuwancin wanda ya janyowa masana’antar matsal akan masu ruwa da tsaki, inda suka bayyana mamaki akan yanayin da har yanzu, bata sake zane ba.

A cewarsu, in har kamfanin na NNPC yaci gaba da zama kamfani mai zaman kansa ta hanyar samar da tsari ba, zai soke dokar da ake da ita a kasa data kirkiro ta, musamman yadda aka zana dokar masana’antar mai, da kamfanin bai samu damar samar da riba ba.

Exit mobile version