Kasar Amurka ta bukaci jami’an diflomasiyarta da ke aiki a birnin tarayya, Abuja, da su fice daga garin domin kaucewa hare-haren ta’addancin da ta ce akwai yiwuwar kai wa.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta gabatar da wannan sanarwa wadda ta bukaci ficewar jami’an diflomasiyyar da ayyukansu ba su zama wajibi ba da su fice tare da iyalansu saboda karfin barazanar da suka ce birnin na fuskanta.
- An Tsaurara Tsaro A Abuja Bayan Gargadin Harin Ta’adanci
- An Zartas Da Kuduri Kan “Gyararren Kundin Ka’idojin JKS”
Ita dai wannan sanarwar ba ta bayyana shirin kwashe jami’an diflomasiyar ba, amma ta yi gargadi ga Amurkawa a kan kauce wa tafiye-tafiyen da ba su zama wajibi ba zuwa Nijeriyar kanta, saboda damuwar da take da ita a kan aikata laifuffuka da kuma rashin kwanciyar hankali.
Wannan gargadin na zuwa ne kwana biyu bayan wadda ta gabatar a karshen mako wadda ke nuni da cewa akwai yiwuwar kai harin ta’addanci a birnin Abuja, kuma tuni wasu kasashen yammacin duniya irin su Birtaniya da Kanada da kuma Australia suka gabatar da irin sa a baya.
Kasar Amurka ba ta yi cikkaken bayani a kan irin barazanar da Abuja da ke dauke da mutane sama da miliyan shida ke fuskanta ba, sai dai masana harkar tsaro na danganta wannan gargadi da karuwar hare-haren ‘yan ta’adda a Nijeriya musamman ganin yadda suka fasa gidan yarin Kuje a watannin baya, suka kuma fitar da wasu abokan aikinsu.
Sai dai hukumar tsaron farin kaya (DSS), ta bukaci jama’a da su kwantar da hankalinsu, inda ta ce tana aiki tare da wasu hukumomin tsaro domin kare lafiyar jama’ar birnin da kuma kasa baki daya.