Dandalin Tuntuɓa na Arewa (ACF) ya yi gargaɗin cewa, ana ƙoƙarin ganin ƙarshen haƙurin Arewacin Nijeriya biyo bayan ta’azzarar matsalar rashin tsaro da talauci da kuma annobar muhalli da yankin ke fuskanta.
Dandalin ya yi wannan gargadin ne a yayin babban taron kwamitin zartarwa na ACF karo na 78 da ya gudanar a Kaduna.
- Sin Ta Shiga Jerin Kasashe 3 Dake Sahun Gaba Wajen Gudanar Da Cinikayya Da Kasashe Da Yankunan Duniya 157
- Harin Asibitin Gaza Ya Halaka Mutane da Dama, Ciki Har da Ƴan Jarida
Shugaban Dandalin, Mamman Osuman, wanda ya yi jawabi a wurin taron, ya ce Arewa ba za ta iya yin shiru ba a yayin da yankin ke fama da irin wannan kalubalen da “ya ƙi ci ya ƙi cinyewa”.
Ya kuma yi gargadin cewa, “Wannan ba lokaci ba ne da Arewa za ta naɗe hannunta tana kallo yayin da al’amura ke ci gaba da taɓarɓarewa, lamarin tsaro yana kara ta’azzara yayin da ake ci gaba da kwashe albarkatun yankin, ambaliyar ruwa na ci gaba da barazana, dole ne mu tashi tsaye mu hada kai domin kare yankin.”
Osuman ya koka da kashe-kashen da ake yi a Arewacin Nijeriya a kullum, yana mai jaddada cewa, babu yadda za a yi, a zura ido ana kallo.
“Mun yi asarar yara, matasa maza da mata, da tsoffi saboda ambaliyar ruwa, bala’o’i, ‘yan bindiga da masu kwacen wayoyi, halin da ake ciki, akwai matukar damuwa, don haka nake kira da a yi tunani mai zurfi kan nemo mafita da kuma addu’a,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp