Tsoro ya haifar da rarrabuwar kawuna a kananan hukumomin Tureta da Dange/Shuni na Jihar Sokoto, yayin da hare-haren ‘yan bindiga ke ci gaba da addabar al’umma, lamarin da ya tilasta wa daruruwan iyalai tserewa daga gidajensu cikin halin kunci.
Tsawon watanni, mazauna yankin – musamman mata da yara – sun yi gudun hijira a cikin dare, suna neman mafaka a buɗaɗɗen wurare, dazuzzuka, da karkashin bishiyoyi, ba su iya kwana a cikin gida saboda ci gaba da barazanar tashin hankali.
- Hukumar NABDA Ta Bukaci Musulmi Su Cire Fargabar Amfani Da Fasahar Alkinta Halittu
- Muhimman Batutuwan Da Za Mu Yi La’akari Da Su Kafin Amincewa Da Bukatun Kirkirar Sabbin Jihohi — Majalisar Dattawa
“Ban shiga gidana ba cikin wata uku,” in ji Halima, wata uwa mai ‘ya’ya hudu daga Tureta.
“Kowane dare, muna kwana a karkashin bishiya, muna rayuwa cikin tsoro, tare da fargabar duk sautin da muka ii ‘yan fashi.”
Zanga-zanga a Zamfara
A halin da ake ciki, mazauna kauyuka sama da 30 na gundumar Dan-Isa da Kagara a Karamar Hukumar Kaura-Namoda ta Jihar Zamfara sun gudanar da zanga-zangar lumana a Gusau babban birnin Jihar a ranar Alhamis.
Sun yi kira da gwamnati ta sa baki cikin gaggawa domin magance matsalar rashin tsaro da ke kara kamari a cikin al’ummominsu.
Masu zanga-zangar wadanda galibinsu mata da yara ne suka yi tattaki a kan titunan Gusau, rike da kwalaye masu dauke da saonni kamar haka: “Muna Bukatar Zaman Lafiya a Kauyukan Kaura-Namoda,” “Ya Kamata Gwamna Dauda Lawal da Matawalle Su Cece Mu,” “Ana Kashe Jama’ar Mu Kullum.
Da yake jawabi ga manema labarai a gaban gidan gwamnati da ke Gusau, daya daga cikin shugabannin al’ummar yankin, Lawal Kamilu daga Dan-Isa, ya bayyana zanga-zangar a matsayin kukan neman taimako bayan shafe shekaru ana kai hare-haren ‘yan fashi, da sace-sace da kashe-kashe.
“Mun fito ne daga kauyuka kusan 30. Mafi yawanmu a nan mata ne da kananan yara saboda yawancin mazajenmu ko dai an kashe su ko kuma ‘yan bindiga sun yi garkuwa da su,” in ji Kamilu.
Martanin gwamnati
martanin da ya mayar, Kanar Ahmed Usman (mai ritaya), mai bai wa gwamnan Jihar Sokoto shawara kan harkokin tsaro, ya amince da zanga-zangar amma ya ce gwamnati na daukar matakan dawo da zaman lafiya.
“Jihar tana ci gaba da gudanar da ayyuka tare da hadin gwiwar jami’an tsaro, wanda aka samu gagarumar nasara,” in ji Kanar Usman.
“Saboda irin namijin kokarin da jami’an tsaronmu na yau da kullum da masu gadin al’umma suke yi, muna hada gwiwa da shugabannin al’umma domin dawo da zaman lafiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp