Shirin Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP) ya yi gargaɗin cewa ƙaruwar hare-hare a Arewacin Nijeriya na iya jefa mutane cikin mummunar yunwa da ba a taɓa gani ba.
Sabbin bincike sun nuna cewa kusan mutane miliyan 35 za su fuskanci matsananciyar yunwa a 2026, wanda shi ne adadi mafi yawa da aka taɓa samu a Nijeriya da ma Afrika baki ɗaya.
- Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Goyon Baya Ga Sake Bincikar Laifukan Da Japan Ta Tafka
- Kano Pillars Ta Samu Nasarar Farko A Wasanni 8 Da Ta Buga
WFP ta ce hare-haren ’yan bindiga sun ƙaru a 2025.
Ƙungiyoyi kamar JNIM da ISWAP na faɗaɗa hare-harensu, ciki har da kai wa sojoji hari da sace ɗalibai.
David Stevenson, daraktan shirin a Nijeriya, ya ce hare-haren suna hana manoma zuwa gonaki, lamarin da ke haifar da ƙarancin abinci a lokutan da buƙata ke ƙaruwa.
A jihohin Borno, Yobe da Adamawa, kusan mutane miliyan shida ne ke fama da rashin abinci.
A Borno kaɗai, ana hasashen mutum 15,000 za su fuskanci matsananciyar yunwa idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba.
Yara a jihohin Sakkwato, Katsina, Zamfara da Yobe na fama da tamowa.
A yanzu kusan mutum miliyan ɗaya ne ke dogaro da taimakon abinci, amma ƙarancin kuɗi ya sa an rage shirye-shirye, lamarin da ya shafi yara sama da 300,000.














