• English
  • Business News
Monday, November 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rasuwar Dantata Babban Rashi Ne Ga Afirka – Atiku

by Sadiq
4 months ago
Dantata

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana rasuwar attajiri kuma mai taimakon al’umma, Alhaji Aminu Dantata, a matsayin babban rashi ba kawai ga Jihar Kano ba, har ma ga Nijeriya da Nahiyar Afirka baki ɗaya. 

Ya yaba da irin gudummawar da Dantata ya bayar wajen bunƙasa tattalin arziƙi da samar da ayyukan yi.

  • Sin Ta Samu Nasarorin A Zo A Gani Wajen Yaki Da Miyagun Kwayoyi
  • Bam Ya Kashe Mutane 4, Ya Jikkata 21 A Yobe

A cikin wata sanarwa daga ofishin yaɗa labaransa, Atiku ya ce ya ji matuƙar baƙin ciki da rasuwar wannan gogaggen ɗan kasuwa wanda ya shahara sosai a Nijeriya da Afirka.

“Aminu Dantata ya kasance sanannen ɗan kasuwa na tsawon shekaru da dama. Ya zaburar da matasa da dama su shiga harkar kasuwanci,” in ji Atiku.

“Ba za a iya tattauna harkokin kasuwanci a Nijeriya ba tare da an ambaci sunan dangin Dantata ba.”

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno

Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya

Atiku, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP a 2023, ya bayyana Dantata a matsayin jarumin da ke ɗaukar kasada a harkokin kasuwanci, wanda ya ce wata muhimmiyar ɗabi’a ce ta manyan masu saka hannun jari.

Ya yaba da yadda Dantata ya sauya kasuwancin danginsu daga saye da sayarwa ta hanyar gargajiya zuwa aikin gine-gine da injiniyanci na zamani, wanda hakan ya samar da dubban ayyukan yi ga ‘yan Nijeriya.

Atiku ya kuma nuna girmamawa ga Dantata bisa irin taimakon da yake yi wa jama’a cikin sirri ba tare da neman ɗaukaka ko yabo ba.

“Ya kasance mai dukiya sosai amma bai taɓa nuna girman kai ba, wannan ɗabi’a ce da ba kowa ke da ita ba,” in ji Atiku.

“Ya kasance abin koyi kuma tushen ƙarfafawa ga mutane da dama.”

Ya ƙara da cewa Dantata mutum ne mai son zaman lafiya wanda ya guji maganganun da ke kawo rabuwar kau, kuma ya jajirce wajen ƙarfafa zaman lafiya a tsakanin ‘yan Nijeriya.

Atiku ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta girmama Dantata ta hanyar sanya sunansa a wani muhimmin gini ko cibiyar gwamnati, domin tunawa da gudunmawarsa ga ci gaban al’umma da tattalin arziƙin ƙasa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Boko haram
Manyan Labarai

Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno

November 10, 2025
Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya
Manyan Labarai

Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya

November 8, 2025
Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi
Manyan Labarai

Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi

November 8, 2025
Next Post
Tarihin Yadda Cinikin Bayi Ya Fara A Nahiyar Afirka (3)

Tarihin Yadda Cinikin Bayi Ya Fara A Nahiyar Afirka (3)

LABARAI MASU NASABA

Matatun mai

Yadda Sojoji Suka Tarwatsa Haramtattun Matatun Mai 14 A Yankin Neja Delta 

November 10, 2025
Jibrin Kofa

Ɗan Majalisar Wakilai, Jibrin Ƙofa Ya Sauya Sheƙa Daga NNPP Zuwa APC

November 10, 2025
Boko haram

Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno

November 10, 2025
Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

November 9, 2025
An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

November 9, 2025
Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

November 9, 2025
Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

November 9, 2025
CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

November 9, 2025
Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

November 9, 2025
Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

November 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.