Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Rasuwar Sheikh Ahmed Lemu: Duniyar Malaman Musulunci Ta Girgiza  

by Muhammad
December 25, 2020
in LABARAI
2 min read
Lemu
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Awwal Umar Kontagora, Minna

 

samndaads

A safiyar alhamis din nan ne Allah ya dauki rayuwar Dakta Sheikh Ahmed Lemu.

Rasuwarsa dai ta girgiza duniyar malaman Nijeriya sakamakon gagarumar gudunmawar da ya bayar a fannin bunkasa ilimin addinin Musulunci.

Sheikh Lemu ya rubuta littattafan addinin musulunci da dama da duniyar musulmi ke anfani da su yanzu.

Shehin malamin ya taba samun lambar yabo ta Sarki Faisal Abdulazeez na Kasar Saudiyya a kan gudunmawar da yake bai wa al’umma a bangaren karantarwa da taimakon jama’a da iya mu’amala da wadanda ba musulmi ba a shekarar 2014,.

Takardar da ta fito daga iyalan marigayin, wadda Sheikh Nuruddeen Ahmed Lemu ya sanya wa hannu ta bayyana cewar mahaifinsu ya rasu sakamakon gajeruwar jinya. A cewar takardar an tsara yi masa jana’iza tun a jiya alhamis da misalin 12 na rana juma’ar cikin garin Minna, inda tuni aka yi hakan.

Da yake ta’aziyya ga iyalan mamacin, sakataren gwamnatin Neja, Ahmed Ibrahim Matane ya nuna kaduwarsa akan wannan rashin.

Ahmed Matane ya bayyana marigayin a matsayin jarumi da ya taka rawar gani wajen karantar da al’umma, wanda ya taimaka wajen samun hadin kai da zaman lafiya a kasa.

Sakataren ya bayyana irin gudunmawar da mamacin ya bayar wajen karantar da addini wanda ya janyo masa kwarjini akan abubuwan da suka shafi addini, “fitattace ne wajen hadin kan al’umma a jiha da kasa da ya sanya shi zama mai shiga tsakani a tsakanin mabiya addinai da kare hakkin dan Adam”, in ji shi.

Sakataren ya cigaba da cewar, ” ayyukan marigayi Sheikh Ahmed Lemu wajen karantar da Addinin Musulunci a kasar nan ne ya ba shi damar samun lambar yabo na Sarki Faisal, wanda karamci ne na duniya a bangaren Addinin Musulunci a shekarar 2014 daga sarkin kasar Saudiya.

Ahmed Matane ya yi addu’ar Allah (SWT) ya karbi bakuncinsa, ya gafarta mai kutakuransa, ya tuna da ayyukan sa na alheri, ya kyautata makwancinsa, ya kuma baiwa iyalansa hakurin jure rashinsa.

Marigayi Sheikh Ahmed Lemu ya taka muhimmiyar rawa wajen yada addinin musulunci a kasa da duniya, inda hakan ya bai wa mabiya addinai damar fahimtar addinin musulunci.

Kafin rasuwarsa ya yi aiki a jihar Sokoto inda daga bisani ya dawo jiharsa ta Neja ya kafa cibiyar yada addinin musulunci mai suna Islamic Education Trust wadda ta zama cibiyar karantarwa da nazarce-nazarcen addinin musulunci a duniya.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Al’ummomi Na Ci Gaba Da Bayyana Kyawawan Halayen Marigayi Sam Nda-Isaiah  

Next Post

Bukatar Yada Kauna Ta Mamaye Sakonnin Kirsimetin Bana

RelatedPosts

Man Fetur

Kudirin Dokar Man Fetur Zai Bai Wa Nijeriya Damar Cin Gajiyar Albarkatunsa – Majalisar Dattawa

by Muhammad
2 hours ago
0

Daga Muhammad Maitela, Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan...

Jobe

Ma’aikata Da ’Yan Fansho Ke Wawashe Rabin Kudin Katsina, Cewar Kwamishina Jobe

by Muhammad
2 hours ago
0

Daga Sagir Abubukar, Kwamishinan Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki...

Rasuwar

Ana Cigaba Da Jimamin Rasuwar Mai Shari’ a Rabiu Danlami A Kano

by Muhammad
2 hours ago
0

Daga Haruna Akarada, Ana cigaba da gudanar da ta’aziyya ta...

Next Post
Kirsimetin Bana

Bukatar Yada Kauna Ta Mamaye Sakonnin Kirsimetin Bana

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version