Ana nuna damuwa kan sahihancin rahotannin kungiyoyin masu sa ido kan zabe, saboda mafi yawancinsu suna nuna son ransu wajen bayar da rahotanni, yayin da wasu kuma ake ke hada kai da su wajen tafka magudin zabe ko su yi biyayya ga iyayen gidansu ko kuma wadanda suke ra’ayinsu.
Zabuka a Nijeriya na cike da masu sa ido da kungiyoyi daban-daban ke turawa. Domin sa ido a babban zaben 2023, an tura masu sa ido na cikin gida da na kasashen waje 146,913. Sannan kimanin 1,000 daga cikinsu ake sa ran za su saka ido zaben gwamnan Jihar Edo.
- Dakta Gadan-ƙaya Ya Bada Haƙuri Kan Zargin Auren Jinsi Da Ya Yi A Bauchi
- Yawan Mutanen Da Suka Shiga Da Fita Daga Kasar Sin A Hutun Bikin Tsakiyar Kaka Ya Zarce Miliyan 5.25
Yayin da akasarin kungiyoyin masu sa ido ba sa gabatar da rahotanni a karshen zabukan, kamar yadda shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa wasu da suka mika rahoton ana tambayar su kan sahihincin rahotannin.
Yayin da yake jawabi ga kungiyoyin farar hula, Yakubu ya ce, “Da yawa daga cikinku da suka gabatar da rahotonsu, har yanzu wasu masu sa ido da aka amince da su ba su yi haka ba a zabukan da ya gabata da zabukan cike gibi da kuma zaben fitar da gwani.
“Don haka zan iya yin amfani da wannan damar don tunatar da wadanda har yanzu ba su gabatar da rahoton bincikensu ba cewa ya zama dole su bayar idan suna so a kara ba su damar sa ido a zaben da za a yi nan gaba.”
Da yake zantawa da LEADERSHIP, ko’odinetan gidauniyar samar da ci gaba mai dorewa, Jude Uzoma, ya yarda cewa rahotannin da wasu kungiyoyin sa ido kan zabuka na hada kai da ‘yan siyasa wajen bayar da rahotonnin da ba su dace ba.
Uzoma ya ce, kamar yadda cin hanci da rashawa ya mamaye dukkan bangarori na rayuwar al’ummar Nijeriya, haka ma yake tasiri wajen sa ido a harkokin zabe.
“Kamar yadda mutane ke cewa, cin hanci da rashawa yana dukkanin bangarorin rayuwarmu, tun daga addini, tattalin arziki, siyasa, kasuwanci da duk wani abu.
“Babu wanda ya kubuta daga cin hanci da rashawa, ciki har da kungiyoyin farar hula da ke aiki da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a matsayin masu sa ido na kasashen waje ko kuma masu sa ido na cikin gida. Wasu kungiyoyin sa ido suna goyi bayan jam’iyyar PDP, yayin da wasu ke goyon bayan APC a lokacin zabe,” in ji shi.
Masana sun tabbatar da cewa masu saka ido a zabe suna da matukar tasiri wajen gudanar da sahihin zabe a Nijeriya, wanda suke bayar da rahotanni inda aka yi dai-dai da inda ba a yi ba.