Wadanda suke da ilimi game da muhimmancin raya al’da, ko kusa, ba su yin kasa-a-gwiwa wajen raya ta, daga lokaci zuwa lokaci. Bugu da kari, batun “raya al’da”, wani abu ne da yake da fadi ainun, wanda ya kunshi duka wani janibi na rayuwar jama’ar gari, kasa, birni, kauye, wani lokaci ma na hade al’ummun nahiya guda, idan aka fadada ma’anar al’dar mutane.
Kamar yadda bayanai ke zuwa daga majiyoyi masu tushe daga tsagin gwamnatin Jihar Kano cewa, akwai wani gagarumin “Bikin Nuna Fasahohi da Al’adun Bahaushen Kano” da Hukumar Tarihi da Al’adu ta Kano ke kan shiryawa karkashin sahalewar mai girma gwamna, Abba K. Yusuf, wanda ake wa bikin take, ko ace lakabi da KANFES “KANFEST, 2025 – KANO FESTIBAL”. Masana da wasu daga masu sharhi a kan al’adar Malam Bahaushe a Kano, sun kalli wannan biki na nuna fasahar Bahaushe da al’adunsa da ake yunkurin gudanarwa a Jihar Kano a cikin wata mai kamawa na Okotoba, 2025, a matsayin wanda ba a taba shirya hatta kwatankwacinsa a Kanon ba. Sun kara da cewa, manyan bukukuwan raya al’dar Bahaushen Kano da ake shiryawa a garin, bai wuce hawan daushe ba. Wanda ya kunshi nuna kayan kawa na dawakai, sukuwa, kade-kade da sauransu.
- Manyan Jami’an Kasashen Afirka Suna Fatan Fadada Hadin Gwiwa Da Kasar Sin
- Jami’an Tsaro Sun Kashe Ƙasurgumin Mai Garkuwa Da Mutane, Maidawa Da Wasu A Kwara
Na’am, wasannin dambe, kokawa da sauran wasannin da ke da jibi da al’dar Bahaushe da ake gani nan da can a kwaryar birni ko a karkara a na shiryawa, gaba daya, ko a ce akasari, ba hukumomi ne ke shiryawa ba. Wannan gagarimin gangankon bikin raya al’adar Bahaushen Kano da ake kokarin shiryawa karkashin gwamnatin Abba Gida-Gida, babu shakka, wata gwamnati a Kano, ta Soja, ko ta Farar-hula, ba ta taba katarin shirya irin bikin ba. Kafin a je da nisa, ko akwai wani alfanu da ake girba karkashin raya al’ada?. Mece ce ma al’adar kanta?.
A takaicen takaitawa, tsarin zamantakewar al’umma, tufafinsu, abincinsu, gine-ginensu, sana’o’insu, addininsu, halaiyarsu da sauransu, duka, sukan taru ne su fassara mutanen da suka yi tarayya cikin wadannan abubuwa da aka zayyano cewa, suna da al’ada iri kaza, ko iri guda. Da mutum zai binciki tarihin Malam Bahaushe, za a iske cewa, tun gabanin zuwan Turawan Ingilishi wannan kasa, yana da kyawawan al’adunsa, son kowa, kin wanda ya rasa. Bayan iya dasisa ta Bature, da kuma sakaci na Bahaushen, sune suka hadu, tare da mantar da Bahaushen al’adar tasa, alhali da yawa daga al’ummun Duniya, na kife ne bisa al’adunsu, wanda a sanadiyyar rikonsu da al’adun nasu ne, fannoni daban-daban na rayuwar yau da kullum, irin su bangaren tattalin arziki, shugabanci, masana’antu, sana’o’i da sauransu suke kan bunkasa nan da nan. Game da wannan batu, kasar Sin a yau, ta ishi mai karatu hujjar samun ci gaba a kowane fanni na rayuwar jama’a, wanda wannan kasa ta Sin ko Chana, na daga kasashen da Duniya ta shaide su, wajen yin riko da al’dar Kaka da Kakanni.
Wasan Kalankuwa A Nijeriya, 1977
A gwamnatance a wannan kasa, an fara shirya manyan bukukuwan nuna fasahohinmu da aladunmu na-dauri, cikin Shekarar 1977 a Legas. Wanda aka fara gudanar da taron, daga 15 ga Watan Janairu, zuwa 12 ga Watan Farairun Shekarar 1977. A farkon lamari, an niyyaci ci gaba da shirya bikin na baje-kolin al’ada ne a duk Shekara, da niyyar samar da hadin-kai a tsakanin jama’ar Kasa bakidaya. Da farko an kira bikin ne da FESTAC ’77, daga baya aka koma kiransa da NAFEST (National Festibal of Arts and Culture).
Saboda muhimmancin irin wadannan bukukuwa, lokacin da aka fara shirya shi a wannan kasa, an sami mahalarta taron ne daga mabanbantan kasashe har kimanin hamsin da biyar (55). Ba ya ga yunkurin samun hadin-kai a tsakanin al’umar wannan kasa, an kara fadada kudirin taron har zuwa ga daukacin sassan duniya. Inda aka nuna cewa, duk wani mutum bakar-fata dake zaune a wannan nahiya tamu ta Afurka, da sauran kasashen Duniya, shi ma wannan taron nuna fasahohin mutane bakaen fata da al’adunsu nasa ne, a matsayinsa na guda daga jinsin bakar fata. Irin wannan wasan Kalankuwa na farko, zai iya tunawa mutumin wannan kasa, yawan kiraye-kirayen da marigayi Dr Yusuf Maitama Sule Danmasanin Kano ke yi cewa, lokaci ya yi da ya dace jama’ar Afurka su tashi su lalubo irin tsarin Dimukradiyyar da ta dace da mutanensu bakaken-fata, tare da rabuwa da irin dimukradiyyar kasashen Turai da Amurka.
Makasudin Shirya Wannan Biki A Kano, KANFEST, 2025
Da mutum zai tsaya ya dubi irin dalilan da masu shirya wannan taro a Kano suka gabatar, lalle zai kai ga fahimtar yiwuwar ciyar da al’uma gaba, da yunkurin raya al’ada ke samarwa. Daga bayanan da ke fitowa daga waccan ma’aikata mai jibi da tarihi da al’adu ta Kano, “History and Culture Bureau”, sun fadi cewa, wannan biki da a turance aka kira shi da “First Kano Festibal of Arts and Culture (KANFEST, 2025), an shirya shi ne bisa wasu manyan makasudai da kuma wasu manufofi da ake son cimmawa. Da farko, wannan hukuma, ta ayyana cewa, ta shirya wannan babban biki ne, don nuna kyawawan al’adu hada da fasahohin da Bahaushen Kano ke da shi, ko a ce ya gada kaka da kakanni. Kuma za a nunawa daukacin al’umar Duniya wannan biki, babu ragin-daka.
Bugu da kari, akwai wasu wasannin nishadi iri daban-daban masu kayatarwa da za a nuna su ga mahalarta taron, da ma waninsu. Wasannin Bahaushe, irin su wasannin Wanzamai, wasan wuta na Makera, wasan shan kankana na Manoma. Sannan, akwai baje-kolin basira daga gwanayen mabanbantan masu sana’o’in Malam Bahaushe, wadanda suma za su zalakarsu a ranakun bikin a Kano. Sana’o’in Majema, Masaka, Marina, Dukawa, da ma tsagin wasanni masu kayatarwa, suma za a nuna su ga mahalarta taron. Wasan “Yan-baka, wasan langa, wasan bago, “yar-carafke, gada, lugude, tafa-tafa, “yar gala-gala, kokawa, dambe, Malam na bakin kogi…da sauransu, duka za a nuna su daya bayan daya.
Tamkar irin yadda aka fara shirya wannan taro a matakin kasa bakidaya a Shekarar 1977, ita ma wannan hukuma da ta shirya taron a Kano, na da kudirin ci gaba da shirya bikin a duk Shekara, tamkar irin yadda manyan kasashen Duniya da suka ci gaba a yau suke shiryawa. Ba ya ga wasannin kwaikwayo na nishadi da ilmantarwa da za a nuna a ranakun bikin, suma kananan yara ba a bar su a baya ba, suma za su zo, tare da baje-kolin irin baiwar da Allah Yai musu. Jama’ar kowace karamar hukuma a Kano, za su halarci wannan biki da ake kokarin gudanarwa. Sannan, kowane 6angare na kananan hukumomin, za su zo tare da nuna irin baiwa, hazaka da fasahohin da suka yi shuhura akai, a ranakun bikin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp