Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Rayuwa Bayan Rabuwar Mata Da Miji

by
4 years ago
in Madubin Rayuwa
3 min read
Rayuwa Bayan Rabuwar Mata Da Miji
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Labarai Masu Nasaba

Aishatu Gwadabe: ‘Yar Arewa Da Take Shuhura A Ƙasashen Duniya

Karin Kudin Lantarki A Nijeriya: Kura Da Shan Duka, Gardi Da Kwashe Kudi  

A wannan gabar batun sun kasu kashi biyu, lokacin da miji ya saki mata, da lokacin da miji ya rasu ya bar mace .To a yau zan yi magana ne a kan rabuwar aure tsakanin miji da mata. Daga lokacin da miji ya saki matarsa daga lokacin za ta fara haduwa da matsaloli daban- daban, musamman idan aka ce ta na da yara hankalinta zai kasu kashi biyu ko da ace ba ta son ci gaba da zama da mijin amma ta ta na so ta rayu tare da yaranta. Sai dai ta bangaren namiji a lokacin zai nuna karfin ikon cewar yara na sa ne shi ya cancanta ya rike su, wani ma har mai shan nono cewa zai yi a ajiye masa dansa ko ‘yarsa mun sha ganin irin hakan. Ba wannan ne kawai matsalar ba wani lokaci akan rasa yaran bayan an raba su da mahaifiyarsu ko su shiga wata dabi’a marar kyau saboda rashin kula. Wannan hali da yaro zai shiga shi zai taba uwar har ya zamo mata matsala a ragowar rayuwarta, wata ma ko wani aure ta yi ba za ta samu kwanciyar hankali da sabon mijin ba saboda kulafucin rabuwa da yaran.
Matsalolin da Ke Biyo Bayan Rabuwar Ma’aurata…
Akwai matsaloli ma su tarin yawa sai dai zan kawo kadan daga cikinsu:
Daga Bangaren Mace:
1. Ya na haifar mata da rashin nutsuwa.
2. Ya na hana ta zaman aure a duk in da ta yi.
3. Ya na haifar ma ta da rashin jituwa tsakanin ta da ‘yan uwanta, ta yadda za su ga ta tsangwami kanta akan yaran da ubansu ya sake ta.
4. A kullum tunaninta zai zama daban ne a kan mai kula da yaran.
Bangaren Miji:
1. Zai zama mai sa ido a kan duk wani abu da ya shafi yaran karshe za a iya samun matsala da mai kula da su (idan mai kula ne kenan).
2. Idan bai dace da mace ta kwarai ba, ba za ta kula da su ba kuma ba za ta bari shi ya kula da su Ba.
4. Ya na sa maigida ya zama mai auri saki.
Bangaren Yara.
Wannan rabuwar mahaifa kan jawo :
1.Yaro kan iya kangare
2. Saboda rashin kula yaro sai ya fada harkar banza kamar sata, shaye-shaye da sauransu.
3. Ya na haifar da rashin jituwa tsakanin matar uba da yaran.
4. Ya na haifar da tsana tsakanin mahaifi da yaran.
5. Ya na haifar da gaba tsakanin wadannan yara da yaran da mahaifiyarsu ke gidan da sauransu.
Ina Mafita?
Mafita a nan ita ce :
1. Mu zama masu hakuri a zamantakewa saboda yaranmu.
2. Maigida idan ya saki mace kar ya raba ta kwata -kwata da yaranta, ya samu lokacin da za a dinga kai mata su a duk in da ta ke.
3. Yara kanana maigida ya yi hawuri ya bar ta da shi har zuwa lokacin da zai mallaki hankalin kansa.
4. A lokacin da aka rabu tsakanin mata da miji, mace ta nutsu ba ta yi fishi ba na kin waiwayar yaran da ta bari.
5. Sannan mace ta rage sa rai akan yaran ta yadda za ta rasa kwanciyar hankali.
6. Ko yan uwanta su ringa zuwa su na duba halin da yaran ke ciki.
7. Maigida Ya sa ido sosai wurin kulawar yaran da mahaifiyarsu ba ta gidan.
8. Idan yaro ya zo da matsala, uba ya tsaya ya saurare shi.
9. Wurin yin hukunci akan wata matsala da za ta taso maigida ya tsaya ya yi bincike sosai kafin yanke hukunci.

Shawara:
Ina kira ga iyaye su ji tsoron Allah, musamman a zamantakewa kar su cutar da junansu domin duk macen da aka raba ta da yaranta an cutar da ita an kuma cutar da yaranta. Su zama masu hakuri da hangen nesa wurin aiwatar da hukunci musamman ta abin da ya shafi rabuwar aure.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Mahimmancin Kankana Ga Lafiyar Dan Adam

Next Post

Hajiya Basira Ibrahim Dantata:Jarumar Tsamo Jama’a Daga Kangin Rashin Abin Yi

Labarai Masu Nasaba

Aishatu Gwadabe: ‘Yar Arewa Da Take Shuhura A Ƙasashen Duniya

Aishatu Gwadabe: ‘Yar Arewa Da Take Shuhura A Ƙasashen Duniya

by
5 months ago
0

...

Lantarki

Karin Kudin Lantarki A Nijeriya: Kura Da Shan Duka, Gardi Da Kwashe Kudi  

by
2 years ago
0

...

Kalubale: Wulakantar Da Sana’o’in Gargajiya Ga ‘Yan Gado

Kalubale: Wulakantar Da Sana’o’in Gargajiya Ga ‘Yan Gado

by
2 years ago
0

...

Cigaban Nazari A Kan Sana’o’in Gargajiya Na Bahaushe   

Cigaban Nazari A Kan Sana’o’in Gargajiya Na Bahaushe  

by
2 years ago
0

...

Next Post
Hajiya Basira Ibrahim Dantata:Jarumar Tsamo Jama’a Daga Kangin Rashin Abin Yi

Hajiya Basira Ibrahim Dantata:Jarumar Tsamo Jama’a Daga Kangin Rashin Abin Yi

Leave Comment

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

Go to mobile version
%d bloggers like this: