Daukar juna ba a bakin komai ba: Da yawan ma’aurata ganin an kwana biyu tare, an saba da juna sai ya zama kar ta san kar ne, su kan manta da abubuwan da kan kara ma zamantakewarsu armashi.
Zai zamo mace duk abin da mijinta zai yi ba za ta ga bajintar shi ba, tana ganin ai dolen shi ne, dan haka ba ta ga abin yabawa ba.
- Gwamnatin Abba Kabir Za Ta Inganta Tsarin Makarantun Tsangayu A Kano – Falaki
- Tattalin Arzikin Sin Zai Ci Gaba Da Zama Injin Farfadowar Tattalin Arzikin Duniya
Haka ta bangaren maza ma, babu wannan yabawar tsakaninsu da matansu. Yana da kyau komin kankantar abu da miji ko mata ta/ya yi, a yaba a kuma gode. Hakan zai kara karfafa wa mutum. Idan girki ta yi, kamata ya yi ka gode ma ta tare da kuranta abincinta, haka bangaren kwalliya ma.
Shi ya sa wasu matan da sun yi aure, duk wata kwalliya sai su zubar, saboda mazajensu ba sa yabawa. Haka ta bangaren hidimar gida, ya kamata mata su rika yabawa mazajensu duk da cewa hakkinsu ne su dauki nauyin iyalansu, amma yana da kyau a gode mu su. Hakan zai kara mu su kwarin gwiwa.
-Dogon buri: Da yawan maza da mata kan shiga gidajen aurensu da dogon buri, suna tunanin babu komai a cikin rayuwar aure face jin dadi. Sun dauka irin rayuwar fina-finai ce da abubuwa na jin dadi da suke gani. Sai dai kash, rayuwa ce mai tattare da kalubale, wata rana zuma wata rana madaci. Dogon burin da ake shiga da shi na daga cikin manyan kura-kurai da ma’aurata ke tafkawa. Sai bayan an shiga a ga akasin abin da ake tsammani, wanda wasu idan an yi sa’a su kan yi hakuri da abin da suka iske, wasu kuwa a lokacin ne fitintinu za su yi ta bullowa.
Ya zama wajibi ga ma’aurata su cire dogon buri a rayuwar aurensu, su rungumi abin da suka tarar da hannu biyu da yakinin cewa canji na faruwa ne daga kan mutum. Kasancewar aboki ko abokiyar rayuwar da wani nakasu a rayuwa ba shi ke nuna cewa rayuwar zamantakewa ta ruguje ba. Kowane Dan’adam tara yake bai cika goma ba. Haka kowane rayuwar aure bai cika dari bisa dari ba, dole a samu tawaya ta wani bangaren.
-Rashin hakuri: Gaba daya rayuwar aure ‘yar hakuri ce, sannan hakuri shi ne ribar zaman duniya. Muna cikin wani zamani da ma’aurata kamar jiran juna suke, kowane a wuya yake dan uwarsa ya yi abu ya zama abin fada da cece-kuce. Kowane ma’aurata suna samun sabani a tsakanin junansu. Wasu kan yi kokari wajen ganin sun gano bakin zare ta hanyar warware matsalolinsu ta hanyar lumana. Wasu kuwa a lokacin ne zage-zage, buge-buge da bakaken maganganu ke kunno kai. Daga nan sai wutar ta kara ruruwa, har ta kai ga abin da ba a so. Wasu ma’auratan koda sune da laifi ya kan zama abu mai matukar wahala su bude baki su bada hakuri. Daga nan sai gardama ta biyo baya. Ko dan zaman lafiya bada hakuri na kashe wutar fitina.
Daga karshe, za mu iya cewa wadannan suna daga cikin manyan kura-kurai da ma’aurata ke yi. Ba kuma suke nan ba. Idan akwai wasu da kuke ganin ya dace su shiga wannan lisaafi, to sai ku saka su.