Cigaba daga inda muka tsaya a makon jiya.
Wannan shi ne darasinmu na karshe cikin tarihin rayuwar Sayyadina Abubakar da ayyukansa na yada addinin Musulunci. In sha Allahu, idan da rai da lafiya, a mako mai zuwa zamu fara kawo muku tarihin rayuwar Sayyadina Umar da ayyukansa na yada addinin Musulunci.
Cigaba Daga Inda Muka Tsaya A Makon Jiya:
Sahabbai sun gamu da taimakon Allah mai yawa, domin kusan a duk yake – yaken da suka je abokan gaba sun fi su yawa, amma karfin imaninsu da Allah da kyakkyawar manufarsu ta kare addininsa ta sanya taimakon Allah ya zamo a gefensu. Misali a yakin da aka fi sani da suna Harbul Yamamah, yawan mayakan Banu Hanifah ya kai mutum dubu arba’in, amma sojojin Khalid Dan Walid sun daure a kan haduwa da su har sai da suka kashe sama da sojoji dubu goma daga cikinsu, sannan suka kai ga Musailimah inda Wahshi ya dara masa kibiya wadda ta halaka shi. Duka duka Musulman da su kayi shahada a wannan yaki ba su zarce dari shida ba. Daga baya kabilar Banu Hanifa sun nemi sulhu bisa ga tilas, Khalid ya rattaba hannunsa a kan wata yarjejeniya da su wadda a bayanta ne suka musulunta baki dayansu. Kafin haka Musulmai sun ganimanci dukiya da bayi masu yawa daga wajensu. A cikinsu har da kuyangar Sayyidina Ali, wato Khaulatu diyar Ja’afar Al Hanafiyyah wacce ita ce ta haifa masa Muhammad wanda aka fi sani da suna Dan Hanafiyyah (daya daga cikin Imamai ma’asumai).
Bayan Kammala Yakin Ridda:
Bayan da Sayyidina Abubakar Radiyallahu Anhu ya hakikance cewa, ya magance matsalar ridda, sai ya mayar da hankalinsa ga fadada daular Musulunci ta hanyar isar da sakonsa zuwa sauran kasashen ketare. Anan ne fa aka gwabza yake – yake tare da sojojin Majusu na Farisa da Kiristocin Sham. Mafi shahara daga cikin yake – yaken da aka yi shi ne yakin Yarmuk, wanda Musulmai kimanin dubu Ashirin da Bakwai (27,000) suka tunkari rundunar Kiristoci mai mayaka dubu Dari da Ashirin (120,000). Musulmai kafin su cimma fagen wannan yaki sun gamu da kishirwa mai tsanani, wadda ta tilasta su yanka rakumansu don su samu ruwan sha. Haka kuma sun samar da sababbin hanyoyi a cikin sunkurmin daji don takaita tafiya.
An ba da labarin cewa, a cikin wannan yakin ne Mahan Sarkin Ruma ya nemi ganawa da Khalid, inda ya nemi ya tozarta Musulmai yana mai cewa, mun samu labarin yunwa ta fitar da ku. Don haka, za mu sallame ku da Dinari goma goma ko wannenku. Za mu kuma ba ku tufafi da abinci, mu kuma ringa aika muku irinsu ko wacce shekara. To, da yake an ce karen bana shi ke maganin zomon bana, Khalid sai ya ba shi amsa da cewa, mu ba abinda ya kawo mu ba kenan. Mu dai a rayuwarmu babu abin da mu ke so kamar shan jinin Dan Adam, sai mu ka sami labarin cewa, jinin Rumawa ya fi ko wane jinin Dan Adam dadi, shi ne mu ka zo mu yake ku domin mu sha. Fadin haka sai cikin gogan da na jama’arsa suka dibi ruwa, ba tare da bata lokaci ba bayan fara yakin Rumawa suka ringa arcewa suna tsoron kar a shanye jinainansu. Nasarar Allah ta sauka ga Musulmai nan take.
Har wayau a wannan yakin ne Sahabbai suka bar wani gagarumin abin tarihi wanda ba’a taba ganin irinsa ba. Domin kuwa an samu ruwa kadan a lokacin tsananin kishi, amma ya kasance ko wannensu yana cewa a kai ma wani dan uwansa Musulmi har sai da wasu daga cikinsu suka mutu saboda kishirwa alhalin suna zadin ‘yan uwansu da wannan ruwa.
Wafatin Sarkin Musulmai Sayyadina Abubakar:
Lokacin da ciwon ajali ya tsananta ga Sarkin Musulmai Sayyidina Abubakar Radiyallahu Anhu, sai ya tara abokan shawararsa daga cikin Sahabbai ya nemi ra’ayinsu dangane da wanda zai gaje shi. Gaba dayansu sai suka ce, mun ba ka gari, ra’ayinka shi ne namu, ko wannensu yana kokarin ya ture ta daga kansa. Ganin haka sai Sayyidina Abubakar ya neme su da su yi masa jinkiri har ya sake yin nazari.
Bayan haka, sai ya aika aka kira masa Abdur Rahman Dan Auf Radiyallahu Anhu ya tambaye shi kai tsaye, mene ne ra’ayinka dangane da Sayyidina Umar Radiyallahu Anhu? Abdur Rahman ya ce, duk inda ka ajiye shi ya wuce nan. Sannan ya kira Sayyidina Usman Dan Affan Radiyallahu Anhu ya tambaye shi, sai ya ce, badininsa ya fi zahiri. Sayyidina Abubakar ya ce masa, ka kyauta ma kanka domin idan ta tsallake shi to ba inda zata fada sai a kanka.
Allah Mai zamani! Mu duba yadda mulki yake abin gudu a wancan lokaci, amma ba da dadewa ba sai duniya ta canza.
A lokacin rasuwarsa, ‘yarsa Uwar Muminai Nana Aishah Radiyallahu Anhu tana zaune a gabansa tana koyi da wani mawaki da yake fadan albarkacin bakinsa game da mutuwa don ta rage wa kanta damuwa. A nan ne Siddiku ya daga kansa ya ce da ita, me ya sa ba za ki karanta in da Allah yake cewa:
“Kuma mayen mutuwa ya je da gaskiya. (Sai a ce masa) Wannan shi ne abin da ka kasance kana bijirewa daga gare shi.” (Suratu Kaf, aya ta 19).
Da ciwonsa ya dada tsananta an nemi izninsa don a kawo masa likita, sai ya ce, “Ai likita ya duba ni.” Aka ce, me ya fada? Ya ce, Ya ce: “Ni mai aikata abin da naga dama ne.” Yana nufin cewa, Allah ya san halin da yake ciki kuma ba zai fasa abinda ya hukunta ba.
Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu ya yi wafati a cikin watan Jimadha Akhir a shekara ta goma sha uku bayan hijira, bayan ya yi shekaru biyu da watanni uku a kan wannan mukami.
To, wane ne sabon khalifan da aka nada a bayansa? Yaya ya gudanar da mulkinsa? Kuma wane irin ci gaba aka samu a lokacinsa? Sai mu je ga Babi na gaba a mako mai zuwa idan Allah ya kaimu. Alhamdulillahi.
Da wannan muka kawo karshen tarihin rayuwar Sayyadina Abubakar da ayyukansa na yada addinin Muslunci. Abin da muka fada dai-dai Allah ya hadamu a ladan, wannan mukayi kuskure kuma Allah ya yafe mana. Amin.
Idan Allah ya kaimu da rai da lafiya, a mako mai zuwa zamu kawo muku tarihin khalifa na biyu, wato tarihin rayuwar Sayyadina Umar da ayyukansa na yada addinin Muslunci. Sai ku kasance damu a duk ranar Litinin cikin wannan jarida mai albarka ta Leardership Ayau.
A karshe mu na rokon Ubangiji Allah ya dube mu da duban rahamarsa, ya ba mu zaman lafiya a Najeriya (musamman yanki Arewa), ya albarkaci wannan aikin namu, yasa al’umma su amfana dashi. Amin.
Za mu dakata a nan, sai makon mai zuwa idan Allah ya kai mu da rai da lafiya, inda za mu kawo mu ku darasin karshe cikin tarihin rayuwar Sayyadina Abubakar da ayyukansa na yada addinin Muslunci. Kada ku manta; ku na tare da dalibinku dan ‘yar uwarku, Mohammed Bala Garba, Maiduguri. 08098331260.