Abba Ibrahim Wada" />

Real Madrid Ba Za Ta Iya Biyan Fam Miliyan 100 A Kan Hazard Ba

Real Madrid ta bayyaan cewa bazata iya biyan kudi har fam miliyan 100 ba domin siyan dan wasan data dade tana nema Edin Hazard kuma zasu zuga dan wasan yayiwa kungiyar tasa ta Chelsea bore akan dole su sauke farashin da suka saka masa domin yasamu damar komawa Madrid din.
A na ganin Real Madrid zata kashe makudan kudade domin siyan ‘yan wasa a wannan kakar sakamakon yadda kungiyar tasha wahala a bana kuma dan wasa Edin Hazard yana daya daga cikin ‘yan wasan da kungiyar take zawarci.
Real Madrid dai ta tabbatar da cewa dan wasa Edin Hazard ya gama yanke shawarar komawa kungiyar a kakar wasa mai zuwa bayan da kungiyar ta shafe shekara da shekaru tana nemansa kuma hakan zaisa suce dole sai Chelsea ta rage farashin da suke bukata tun farko.
Shi ma dai dan wasan ya dade yana fatan ganin yakoma kungiyar domin buga wasa sai dai kawo yanzu dai ita kanta kungiyar ta sa ta Chelsea ta hakura dashi bayan data fahimci cewa gaba daya zuciyarsa tana Real Madrid amma kuma ta ce dole sai Real Madrid ta biya fam miliyan 100 akan dan wasan dan asalin kasar Belgium.
Real Madrid dai ta ware makudan kudade wajen siyan manyan ‘yan wasa domin tunkarar sabuwar kaka mai zuwa bayan da kungiyar batayi kokari ba a wannan kakar inda tuni akayi waje da ita a gasar cin kofin zakarun turai da kofin Copa Del Rey kuma barcelona ta basu tazarar maki 12 a gasar laliga.
Hazard ne dai ya zura kwallaye biyun da suka bawa kungiyar Chelsea nasara a wasan da suka fafata da kungiyar Westham a ranar Litinin a gasar firimiya kuma yanzu sun koma mataki na uku yayinda kuma a gobe zasu buga gasar cin kofin Yuropa.

Exit mobile version