Connect with us

WASANNI

Real Madrid Ta Amince Da Siyan Aspas Daga Celta Vigo

Published

on

Rahotanni daga kasar Sipaniya sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta amince da siyan dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Celta Vigo, Iago Aspas idan har bata samu damar siyan Rodrigo Moreno ba daga Valencia.

Tun bayan tafiyar Cristiano Ronaldo zuwa Juventus  Real Madrid take zawarcin dan wasan gaba wanda zai maye mata gurbinsa amma kuma har yanzu bata samu ba bayan da Hazard yace bazai koma kungiyar ba.

A ranar 31 ga watan Agusta za’a rufe kasuwar siye da siyar da ‘yan wasa a kasar Sipaniya kuma har yanzu kungiyar bata siyi kowanne dan wasan gaba ba wanda zai maye mata gurbin Ronaldo ba wanda aka siyar fam miliyan 105.

Kamar yadda wasu rahotanni suka bayyana kungiyar Celta Bigo ta yiwa dan wasan fam miliyan 36 yayinda har yanzu farashin Moreno yake fam miliyan 126 farashin da Real Madrid take ganin yayi mata tsada.

Hakan yasa Real Madrid ta mayar da akalarta zuwa ga neman dan wasa Aspas wanda tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ne a baya kafin yakoma kasar ta Sipaniya da buga wasa kuma ya wakilci kasar Sipaniya a gasar cin kofin duniya.

Iago Aspas, mai shekara 31 a duniya, ya buga wasanni 306 kuma ya zura kwallaye 121 sannan kuma ya taimaka aka zura kwallaye 36 a tsawon zaman da yayi a kungiyar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: