Sani Hamisu" />

Red Cross Ta Bada Kyautar Kayan Aiki Ga Manoma 26,000 A Borno

Kwamitin Red Cross na duniya a ranar Litinin ya rarraba tsaba da kuma  kayan aikin gona da kayan abinci ga manoma 26,000 a Jihar Borno.

Bisa ga bayanin ICRC, wannan shirin yana nufin kara gina tattalin arziki na al’ummar da kungiyar Boko Haram ta sanya su gudun hijira har ta kai ga sun rasa muhallin su.

Da yake jawabi a kan rarraba kayyayyaki  a Maiduguri, wakilin tsaron Tattalin Arziki na kungiyar, Cadassou Samuel, ya ce sun yi la’akari da yana yin da yankunan suke cikin na rashin zaman lafiya,wanda kungiyar  Boko Haram ta sanya jama’ar jihar,inda suka yanke shawarar taimakawa mazauna yankin da kayan aikin gonaki domin su samar da abinci ga iyalan su.

Sama’ila ya ce manoman 16,000 a yankin Monguno suka samu wannan kyauta da aka rarraba, yayin da a Maiduguri da Jere mutum  10,000 manoma sun amfana.

Ya ce abubuwan da aka rarraba wa manoma sun hada da shinkafa, dafiya, masara, gero da kuma sorghum tsaba don  samar da kayan aikin gona a gare su.

Ya ce, “Mun rarraba kayan abinci irin su shinkafa, wake da man fetur ga manoma. Wannan ICRC ta yi don kare manoma daga cin abincin da aka rarraba su don noma. “

Ya bayyana cewa, wasu yankunan da rikicin yafi shafa a jihar za su taimaka musu sosai.

Exit mobile version