Uwargidan shugaban kasa, Misis Oluremi Tinubu a ranar Litinin a Abuja, ta kama aiki a ofishinta na matsayin uwargidan shugaban Nijeriya.
Misis Tinubu ta samu rakiyar mataimakanta kan harkokin tsaro, inda ta samu kyakkyawar tarba daga Tijjani Umar, babban sakatare a fadar gwamnatin da kuma wasu manyan jami’ai daga ofishin uwargidan shugaban kasa.
Da isarta bangaren uwargidan shugaban kasa, Misis Tinubu ta yi rangadi a sassa daban-daban da ke cikin bangaren.
Ta fara daga Rukunin Gudanarwa, ICT, Yada Labarai, da masu iso. Ta fara sabawa da ma’aikatanta da ke kowanne bangare ya zuwa yanzun.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp