Uwargidan shugaban kasa Oluremi Tinubu, ta sauya sunan babban dakin taron ‘Maryam Babangida National Centre for Women Development’ zuwa sunan Dr. Maryam Abacha, matar tsohon shugaban kasa a mulkin soja, marigayi Janaral Sani Abacha.
Zauren wanda a da ake kira da ‘African Peace Mission Hall’, uwargidan shugaban kasar ce ta kaddamar da shi kuma aka canza masa suna zuwa Maryam Abacha, saboda irin gudummawar da ta bayar wajen samar da zaman lafiya a nahiyar Afrika.
A jawabinta, uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta ce taron muhimmi ne a kokarin hadin gwiwa wajen karfafa alaka tare da bunkasa ci gaban da aka samu wajen samun hadin kai da dawwamammen dangantaka a tsakanin mata.
Ta bayyana Maryam Abacha a matsayin mace mai hazaka kuma jajirtacciya wajen ci gaban nahiyar Afrika baki daya.
“Shawararta ne ya samar da ma’aikatar harkokin mata ta tarayya tare da nada mace a matsayin minista, wanda hakan ya fadada zuwa jihohi daban-daban tare da girmama al’amuran matan Nijeriya.
“A kwanan nan a yayin sauya sunan wannan cibiya, na jaddada wa mata cewa su dinke barakar da ke tsakaninsu, su nuna halaye masu kyau da kuma mayar da hankali fiye da bambance-bambancen da ke tsakaninmu, kasancewar hadin kan mu a matsayin mata ya fi muhimmanci. Wannan taron yana da mahimmanci a yayin da ya zama babban dama na kafa tarihi wajen samar da dawwamammen zaman lafiya a cikin al’ummarmu.
“A yayin cimma burinmu, yana da kyau mu fahimta tare da karrama mutanen da suka taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa da zaman lafiya da kwanciyar hankali.”
Bayanin na uwargidan shugaban kasar ya yi daidai da tunanin sauran masu jawabi a wurin taron, ciki har da Darakta Janar na cibiyar, Misis Asabe Vilita Bashir, da Sakatariyar Ma’aikatar harkokin mata, Misis Monilola Udoh.
Dukkanninsu sun yi murnar yadda mata ke samun tagomashi a gwamnatance a fagen sake gina kasa.
A nata jawabin, Dakta Maryam Abacha ta yi addu’a ga kasar nan da kuma wannan gwamnati mai ci a karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Tinubu da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima akan Allah ya ba su ikon cimma nasara.
Ta ce galibin matan da ke rike da madafun iko a yau suna da ilimi sosai, inda ta shawarce su a kan su yi amfani da damar da suka samu wajen yin ci gaban al’umma.
Ta yi fatan cewa uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu za ta yi aiki mai kyau.
Ta kuma ba da shawarar cewa ya kamata a karfafa wa dukkan mata gwiwa su zama masu amfani da kuma dacewa wajen ci gaban kasa.
“Ina so na roke ku da cewa ka da a bar mace a baya wajen daukar nauyi. Na yi farin ciki da na kasance jigo wajen kafa wannan cibiya kuma ina godiya ga uwargidan shugaban kasa da cibiyar bisa ganin na cancanci a sanya sunana a wannan katafaren gini haka”.
“Zan tattaro wasu tattaunawarmu da wasu ayyukanmu a cikin kundi kuma ina ƙarfafa ku da ku zama masu ƙwazo domin a zamaninmu, yawancin mu ba mu kammala karatun digiri ba. Mun yi iya bakin kokarinmu muka bar sauran amma yanzu muna da wadanda suka samu ilimi da wayewa da za su kai ‘yan Nijeriya mafi kyawun wuri ga mata”.
Taron ya kasance babban wuri wajen bayyana bayanan zaman lafiya da goyon baya a tsakanin mata.