Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaron Kasa, Malam Nuhu Ribadu ya ba da tabbacin zai halarci babban taron Kamfanin LEADERSHIP na hadin gwiwa da NDLEA kan yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi da sauran miyagun laifuka da rashin tsaro da kuma ci gaban kasa, a matsayin shugaban taron.
Taron mai taken, ‘Shan Miyagan Kwayoyi, Manyan Laifuka, Rashin Tsaro da Ci Gaban Kasa,’ wanda aka tsara gudanarwa a ranar 3 ga Agusta, 2023 a Babbar Cibiyar Taro ta Kasa da Kasa da ke Abuja, wani sabon yunkuri ne na shawo kan yawaitar bazuwar miyagun kwayoyin da ake fama da ita.
- Yarjejeniyar Saukaka Zuba Jari Za Ta Bunkasa Tattalin Arzikin Duniya Da Dala Triliyan 1
- Tinubu Ya Ba Da Umarnin Fitar Da Takin Zamani Da Hatsi Don Rage Radadin Cire Tallafin Fetur
Wata sanarwa da hukumar gudanarwar Rukunan Kamfanonin LEADERSHIP, mai dauke da sa hannun babban edita kuma babban mataimakin shugaban kamfanin, Mista Azu Ishiekwene, ta bayyana cewa kamfanin jaridun tare da hadin gwiwar hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) sun dauki nauyin gudanar da taron ne, “domin samar da mafita kan matsalar a wannan zamani da ake kara bullo da sabbin fasahohi da hanyoyin safara da rarraba miyagun kwayoyin.”
Ishiekwene ya kara da cewa taron na da nufin tattauna makomar yaki da miyagun kwayoyin ne bisa la’akari da yadda za a yi garambawul ga dokokin Nijeriya game da mallaka, amfani, hukunci, tarbiyyantarwa da kuma sake maido da wadanda kwaya ta tagayyara kan turba mai kyau.
“Kamar yadda binciken da Majalisar Dinkin Duniya ta yi kan amfani da kwayoyi a shekarar 2017, ya bayyana bisa kiyasi na adadin al’ummar Nijeriya miliyan 98, akwai miliyan 14.3 da ke amfani da miyagun kwayoyi.
“Wadannan alkaluma sun ninninka ba kawai bisa la’akari da karuwar jama’a da kuma yawan kalubalen zamantakewa da tattalin arziki ba, kai har ma da karuwar ta’addanci, fashi da makami, garkuwa da mutane, da sauran munanan laifuka. Wannan abu ne mai ban tsoro kuma yana bukatar gudunmawa ta gaggawa daga dukkan masu ruwa da tsaki a bangaren shugabannin Nijeriya da masu kishin kasa da kuma kamfanoni,” in ji sanarwar.
Ribadu, wanda ya kasance jagoran yaki da cin hanci da rashawa kuma shugaba na farko a hukumar yaki da masu zamba cikin aminci da karya tattalin arzikin kasa (EFCC), zai gabatar da jawabin bude taron a matsayinsa na shugaban taron.
Sanarwar ta kuma yi nuni da cewa, sabon mai ba wa shugaban kasar shawara a kan harkokin tsaron kasa (NSA) da ya zama na farko da aka nada a mukamin ba tare da ya taba yin aikin soja ba, tun bayan komawar mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999, zai kara tagomashi kan abubuwan da za a tattauna a taron sakamakon yadda a aikace ya fahimci dabarun tattara bayanan sirri da yaki da laifuffuka a lokacin da yake EFCC har ya yi suna a duniya ta wannan fuskar tare da samun lambobin yabo.
Ta kuma kara da cewa, a bisa la’akari da bukatar gaggauta kawar da barazanar shan muggan kwayoyi da ta’addanci, fashi da makami, da yadda abin ke illata ci gaban kasa, taron na hadin gwiwa tsakanin LEADERSHIP da NDLEA ya kudiri aniyar fayyace sabbin hanyoyin sarrafa kwayoyin, da fataucinsu da rarraba su, da kuma yin tambayoyi kan kokarin da hukumomin da ke sahun gaba a yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyin ke yi, tare da sake jaddada kiran shigar al’umma cikin lamarin.
Daga cikin manyan bakin da za su halarci taron akwai wadanda za su zo daga fadar shugaban kasa, majalisar dokoki ta kasa, sojoji, gwamnatocin jihohi, ma’aikatu da hukumomin gwamnati, sarakuna, jami’an diflomasiyya, hukumomin duniya, kamfanoni masu zaman kansu, malamai, kungiyoyi, Ofishin Majalisar Dinkin Duniya Mai Yaki da Miyagun Kwayoyi da Laifuffuka (UNODC), Sakatariyar Tarayyar Afirka da Ofishin Mai Ba Da Shawara Kan Tsaron Kasa (ONSA) da dai sauransu.