Kungiyar kwadago ta yi gargadin cewa za a iya tilasta mata daukar matakan da za su iya kawo cikas ga ayyukan tattalin arzikin kasa nan, wanda ta yi barazanar shiga yajin aiki matukar ba a janye dokar ta-ɓaci a da kakaba a Jihar Ribas cikin gaggawa.
kungiyar ta dai fitar da barazanar ce a cikin wata sanarwa da shugabanta na Jihar Ribas, Aled Agwanwor da shugaban kungiyar ‘yan kasuwa ta jihar, TUC, Ikechukwu Onyefuru da shugaban majalisar tattaunawa ta hadin gwiwa (JNC), Chuku Emecheta.
- ‘Yansanda Sun Hana Hawan Sallah A Kano Saboda Tsaro
- Yadda Ake Fitar Da Zakkar Fidda Kai Da Sallar Idi
kungiyoyin kwadago sun nuna damuwarsu game da shari’a da tasirin tattalin arziki da kuma ayyana dokar ta-ɓaci ta Shugaba Bola Tinubu ya kakaba a Jihar Ribas.
Sun bayyana cewa ayyana dokar ta-vaci da kuma dakatar da zavavven gwamna, Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Odu da mambobin majalisar jihar a matsayin wanda ya sava dokan kundin tsarin mulkin Nijeriya.
Shugabannin kwadago sun dage cewa mutanen Jihar Ribas sun zavi wadannan jami’an ne cikin ‘yanci, kuma duk wani yunkuri na cire su da ya sava wa kundin tsarin mulki yana lalata dimokuraɗiyya.
A cewar shugabannin Ƙwadago, dole ne a sauya irin wadannan lamari don kare mutuncin tsarin dimokuradiyya a Nijeriya.
Sun jaddada wahalar da dokar ta-ɓaci ta haifar wa ma’aikatan kananan hukumomi, da yawa daga cikinsu har yanzu ba su karɓi albashinsu ba.
Sanarwar ta lura cewa hana albashin ma’aikata ya jefa su cikin matsin tattalin arziki, musamman ma a irin wannan lokaci da ake samun tsadar rayuwa a cikin kasar nan.
Ƙungiyar Ƙwadago ta yi gargadin cewa dokar ta-vaci na iya haifar da mummunan sakamako na tattalin arziki, tana mai jaddada muhimmancin da Jihar Ribas ke da ita ga tattalin arzikin Nijeriya da yankin Neja Delta gaba daya.
Ta ce da ma can kasar nan ta riga ta fuskanci hauhawar farashi, raguwar darajar naira, tsadar musayar canji, rashin aikin yi da tsadar rayuwa, rashin kwanciyar hankali a Jihar Ribas na iya kara ta’azzara halin da ake ciki a duk fadin kasar nan.
Sanarwar ta kuma nuna cewa rashin tabbas na siyasa da dokar ta-ɓaci ta haifar ya kori masu saka hannun jari wadanda suka nuna sha’awar zuba hannun jari a tattalin arzikin jihar.
“Wannan asarar saka hannun jari yana lalata kudaden shiga na cikin gida na jihar (IGR), kuma zai yi tasiri na dogon lokaci a ci gaban tattalin arziki da kuma damar samar da ayyukan yi a yankin.
“Duk da cewa mun amince da bukatar kiyaye doka da oda, dole ne a aiwatar da irin wadannan matakai a cikin tsarin kundin tsarin mulkin Nijeriya.
Dakatar da zaɓaɓɓun jami’ai da lalata tsarin biyan albashin ma’aikata ya keta hakkoki dan’adam wanda zai iya ta’azzara rashin tsaro da kalubalen tattalin arziki.
“Ya kamata gwamnatin tarayya ta ba da fifiko ga tsaro da jin dadin ‘yan kasa a kan muradun siyasa.
“Duk wata hanyar mulki da ke sadaukar da jin dadin ma’aikata don ayyukan siyasa zai kara tashin hankali da rashin kwanciyar hankali ga al’umma,” in ji ƙungiyar ƙwadago.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp