Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Richard Horton: Kin Jinin Sin Yunkurin Sauya Tarihi Ne

Published

on

Babban editan mujallar lafiya ta Lancet Dr. Richard Horton, ya ce kin jinin da wasu ke nunawa kasar Sin game da yaduwar cutar COVID-19, kokari ne kawai na sauya tarihi, da kawar da kai daga gazawar kasashen yamma wajen shawo kan wannan annoba.

Dr. Horton ya ce matakan kin jinin Sin na kara kazanta, inda a yanzu suke haifar da yanayi maras kyau, lamarin da ke haifar da nuna wariyar launin fata, da kin jinin wasu al’ummu, matakin da ke barazana ga zaman lafiya da tsaro a matakin kasa da kasa.
Jaridar Birtaniya ta “The Guardian” ta rawaito kalaman na Dr. Horton, yana mai cewa a wannan muhimmin lokaci, ya fi dacewa a maida hankali wajen aiki tukuru maimakon raunana kokari, a kuma kyautata cudanyar dukkanin sassa a fannin yaki da wannan annoba, da fadada fahimtar juna tsakanin al’ummu.
Daga nan sai ya bayyana Sin mai jama’ar da ta kai biliyan 1.4 a matsayin kasa da ita ma ke fuskantar kalubalen tattalin arziki, wanda ke addabar dukkanin duniya. A don haka bazuwar cutar COVID-19, a cewar Dr. Horton, ta haifar da bukatar hadin kan dukkanin al’ummun duniya, maimakon saka kafar wando daya tsakanin gwamnatoci. (Saminu Alhassan)
Advertisement

labarai