Babban bankin Nijeriya (CBN) ya kara yawan adadin kudin da daidaikun mutane ko kungiyoyin za su iya cirewa a mako guda.
Sabon matakin na CBN ya yi nuni da cewa daidaikun mutane za su iya cire kudi har zuwa naira dubu dari biyar (500,000) a cikin mako guda.
Kazalika, sabon matakin ya nuna cewa kungiyoyi za su iya cire naira miliyan biyar a mako.
Idan za ku iya tunawa a sabon tsarin fasalin kudi da CBN ya fitar a kwanakin baya, ya ce daidaikun mutane za su iya cire naira dubu dari N100,000 ne kacal a mako lamarin da ya janyo suka da bore daga wajen al’ummar kasa.
Babban bankin ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwar da ya aike wa bankuna a ranar Laraba.
Kazalika, CBN ya ce, daukan wannan matakin ya biyo bayan sauraron bayanai da ra’ayoyin masu ruwa da tsaki ne kan wannan matakin.